![Sakonnin Masu Karatu (2009) (13)](https://babansadik.com/wp-content/uploads/2017/04/tambayoyi.png)
Sakonnin Masu Karatu (2009) (13)
Ci gaban sakonnin masu karatu. A sha karatu lafiya.
Makaloli a fannin kimiyya da fasaha!
Ci gaban sakonnin masu karatu. A sha karatu lafiya.
Ci gaban sakonnin masu karatu. A sha karatu lafiya.
Ci gaban sakonnin masu karatu. A sha karatu lafiya.
Ci gaban sakonnin masu karatu. A sha karatu lafiya.
Sabanin yadda nayi alkawari cikin shekarar da ta gabata cewa a duk mako zan rika buga sakonnin tes ko na Imel da masu karatu ke aikowa, tare da amsa su, hakan bai faru ba saboda shagala irin tawa. Da fatan za a min hakuri kan abin da ya wuce, kuma zan ci ga da ganin cewa na lazimci wannan dabi’a, don tafi sauki. A yau zan amsa dukkan sakonnin tes da kuka aiko a baya, sannan kuma a makonni masu zuwa in ci gaba da bin tsarin da nayi alkawari.
Kamar kullum, muna mika godiyarmu ga dukkan masu aiko da sakonnin godiya da gamsuwa, da masu bugo waya don yin hakan su ma; musamman ganin cewa baza mu iya ambaton sunayensu ba, saboda yawa da kuma maimatuwan hakan a lokuta dabam-daban. Mun gode matuka.
A yau ma ga mu dauke da wasu cikin wasikun masu karatu. Kamar yadda muka sha fada kwanakin baya, cewa za mu daina amsa maimaitattun tambayoyi, don kauce wa tsawaitawa. Duk wanda ke son yin tambaya, in da hali, zai dace ya binciki kasidun baya da ke mudawwanar wannan shafi a http://fasahar-intanet.blogspot.com, don samun gamsuwa. A halin yanzu ga wadanda kuka aiko mana nan makonnin baya:
Daga wannan mako in Allah ya yarda zamu rika kawo wasikun da kuke aiko mana iya gwargwadon hali, don kauce wa taruwansu. A nan zamu rika amsa wasu cikin tambayoyin da kuke yi, tare da nuna godiya kan wadanda kuka aiko don nuna gamsuwarku. Sai a ci gaba da kasancewa tare da mu.
Ga kadan cikin wasikun masu karatu nan kamar yadda muka saba kawowa lokaci-lokaci. Wasu na riga na amsa su tun sadda aka aiko su, wasu kuma nayi alkawarin amsa su ne a wannan shafi; wasu sakonnin kuma ta hanyar wayar tarho aka yi su, na bayar da amsarsu nan take. Don haka wadanda aka bugo don yabo, sai dai muce Allah saka da alheri, don ba zan iya kawo dukkansu ba. Wadannan sakonni dai na text ne ko wadanda aka rubuto ta hanyar Imel, muna kuma kara nuna godiyarmu ga dukkan masu bugowa ko aiko da sako ta dukkan hanyoyin, Allah saka da alheri, ya kuma bar zumunci, amin summa amin. A halin yanzu ga sakonnin nan:
Bayan dawowa daga hutun Sallah na lura muna da kwantai na wasikun masu karatu wadanda bamu amsa su ba, wadanda kuma suna dauke ne da tambayoyi masu ma’ana. Don haka wannan mako zamu dulmuya hannunmu ne cikin taskar wasikunku, don amsa tambayoyi masu ma’ana, masu kuma saukin amsawa. Wadanda suka ta bugo waya daga birnin Ikko da sauran biranen Arewa kuma muna mika godiyarmu da zumunci; Allah biya ku, amin. A mako mai zuwa kuma sai mu shiga wani fannin. A yanzu ga wasikun naku nan: