Bayani Kan Ɓangarorin Wayar Salula da Dalilan Tsada ko Araharta (8)

Ɓangarorin SoC

Daga cikin kamfanonin da suke samar da nasu na’urar sarrafa bayanai dai har wa yau akwai kamfanin Huawei mai nau’in HiSilicon, zubin Kirin 9000. – Jaridar AMINIYA, Jumma’a, 22 ga watan Satumba, 2023.

232

Babbar Cibiyar Sarrafa Bayanai (SoC)-3

Modems: 

Daga cikin aikin na’urar Modem shi ne, idan ka tashi amfani da rediyon dake wayar, wannan na’ura ce ke taimaka maka wajen kamo tashar rediyon – ya Allah ta Intanet ne, ko kuma kai tsaye, kamar tashar FM misali.  Daga kan fasahar Wi-Fi dake taimakawa wajen kamo siginar Intanet, da fasahar bulutud, da Infirared, da iya amfani da yanayin sadarwar Intanet irin su 3G, da 4G LTE, da 5G, duk aikin wannan na’ura ne gudanar da hakan.  Abin da kuma take yi shi ne, karɓan bayanan da take tattarowa ta hanyar siginar rediyo, sannan ta jirkita su zuwa nau’insu na asali; idan sauti ne, ta jirkita su zuwa sauti.  Idan rubutu ne, kai tsaye za ta jirkita su zuwa rubutattun bayanai.  Idan hotuna ne ta ɗauko daga Intanet, nan take bayan ta karɓe su, za ta jirkita su zuwa yadda ta karɓo su a asali.  Haka lamarin yake wajen taswira, da lambobi, da tambari, da ramzi na dukkan wani irin bayanai.

Waɗannan, a taƙaice, su ne ɓangarorin dake ɗauke kan wannan na’ura ta wayar salula mai suna SoC, ko System-on-Chip.  Kuma yadda bayani ya gabata a makon jiya, dukkansu a dunƙule suke cikin fallen na’ura ƙwaya ɗaya mai marfi a samansa.  Shi yasa na kira ta da suna: Babbar cibiyar sarrafa bayanai na wayar salula.

Gabanin wannan lokaci ko zamani na ƙere-ƙere, ana ƙera dukkan waɗannan na’urori ne daban-daban, sannan a jona su a kan injin wayar salula.  Haka ma lamarin yake dangane da kwamfuta.  To amma shekaru sama da 15 da suka gabata sai tsarin ya canza, inda aka samu kamfanonin da suka gudanar da bincike na musamman kan hikima da dabarun haɗe waɗannan na’urori kan fallen na’ura ɗaya, tare da rage adadin kuɗin da ake kashewa wajen ƙera su daban-daban.  Daga cikin fa’idar da haɗe su wuri guda ya samar har wa yau akwai rage cunkoso cikin injin wayar salula.  Sai dai kuma, wasu kamfanoni ne suka fara wannan aiki?  Samun amsar wannan tambaya zai taimaka mai karatu matuƙa wajen sanin manyana dalilan tsada ko arahar wayar salula ta la’akari da nau’in na’urar SoC da wayar ke ɗauke dashi.

ARM Holdings: 

Kamfanin farko da ya fara samar da SoC dai shi ne kamfanin ARM Holdings dake ƙasar Ingila ko Burtaniya.  Wannan kamfani ne ke zana asalin na’urorin a kan fallen na’ura guda, sannan ya shigar da dukkan umarnin da za su taimaka wajen gudanar ayyukan da bayanansu suka gabata a baya.  Wannan kamfani ne ya fara samar da na’urar CPU na farko a kan SoC mai suna Cortex, a jerin na’urorinsa na CPU mai suna: Cortex A Series.  Kuma shi ne kamfanin da ya fara baiwa kamfanonin ƙera wayar salula lasisin amfani da wannan na’ura a kan wayoyinsu, kafin wasu daga ciki su fara samar da nasu ta amfani da fasahar da kamfanin ya samar.

- Adv -

Qualcom: 

Kamfanin Qualcom ne a gaba wajen shahara a wannan fanni ta ɓangaren wayar salula, kamar yadda kamfanin Intel yake wajen samar da na’urar CPU a ɓangaren kwamfutoci.  Kamfanin farko da ya fara amfani da na’urar CPU ɗinsa mai suna: Snapdragon dai shi ne kamfanin HTC, inda ya ɗora wannan na’ura a kan shahararriyar wayarsa ta salula mai suna: HTC Tattoo, a shekarar 2007.

NVIDIA: 

Bayan kamfanin Qualcom sai kamfanin Nvidia, wanda ke ƙera na’urar CPU mai suna Tegra.  Ya fara hakan ne a shekarar 2009, inda ya fitar da Tegra 1 zuwa Tegra 3, tsakanin shekarar 2009 zuwa 2011.

Daga baya sai kamfanonin wayar salula su ma suka shiga wannan harka na ƙera na’urorin sarrafa bayanai, duk da cewa asalin fasahar dai duk daga kamfanin ARM Holdings suke karɓar lasisi.  Kamfanonin da suka shigo cikin wannan harka dai sun haɗa da kamfanin Samsung, masu na’urar Exynos mai ɗauke da asalin CPU ɗin kamfanin ARM mai suna Cortex A.  Sai kamfanin Mediatek, wanda ke ɗauke kan galibin wayoyin Tecno da Infinix da iTel, da wasu daga cikin wayoyin Samsung, da Sony, da dai sauransu.  Ana cikin haka sai ga kamfanin Apple na ƙasar Amurka, inda ya fitar da nashi masarrafar na musamman mai suna: Apple A4, wanda shi ma dai daga fasahar kamfanin ARM ne.  Kamfanin Apple dai ya fara ƙera nasa na’urar ne tun daga kan iPhone 5.  Ya zuwa yanzu, bayan samar da na’urar CPU da kwafa daga na kamfanin ARM, kamfanin Apple ya ƙara samar da na’urar sarrafa hotuna nasa na kansa wanda ya kira da suna: Apple GPU.  Sannan ya ci gaba da inganta na’urar CPU ɗinsa.  Yanzu haka na’urar CPU nau’in Apple A16 ne ke kan wayarsa ta iPhone 14 Pro Max.

Daga cikin kamfanonin da suke samar da nasu na’urar sarrafa bayanai dai har wa yau akwai kamfanin Huawei mai nau’in HiSilicon, zubin Kirin 9000.  Ba ga wayoyin da yake ƙerawa kaɗai ba, kamfanin Huawei na baiwa wasu kamfanin ma lasisin amfani da fasaharsa ta Kirin.  Bayan kamfanin Huawei, sai kamfanin Google, wanda bai jima ba da shigowa cikin harkar.  Shi kuma ya ƙera na’urar sarrafa bayanai ga wayoyinsa na Google Pixel mai suna: Tensor G-2.  Mahangar kamfanin Google wajen samar da wannan fasaha tasa dai shi ne don taimaka wa wayoyinsa wajen ta’ammali da dandazon bayanai masu ɗimbin yawa don samun abin dogaro ga fasahar AI da ya ɗora wayoyinsa akai.

A taƙaice dai, samuwar waɗannan na’urorin sadarwa tsakanin kamfani da zubi da kuma nau’ukansu, na daga cikin manyan dalilan dake sa wayar salula tsada ko araha.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.