Bayani Kan Ɓangarorin Wayar Salula da Dalilan Tsada ko Araharta (6)

Ɓangaren "System on Chip"

Ɓangaren SoC ya ƙunshi manyan na’urori guda bakwai ne.  Waɗannan na’urori dai su ne ke da alhalin tafiyar da sauran ɓangarorin wayar salula.  Shi yasa ma wasu masana ke cewa, cibiyar SoC ce ƙwakwalwar wayar salula.  – Jaridar AMINIYA, Jumma’a, 8 ga watan Satumba, 2023.

205

Babbar Cibiyar Sarrafa Bayanai (SoC)

Wannan ɓangare shi ake kira: “System-on-Chip”, ko “SoC” a gajarce.  Kuma kamar yadda muka bayyana a makon jiya, wannan ɓangare ne ke lura da dukkan ayyukan wayar salula; daga sadda ka kunna zuwa sadda za ka kashe wayar, duk wani umarni da kake bata, duk wani abin da za ka maƙala mata, ko za ka kalla a shafi ko fuskar wayar, ko za ka rubuta, ko za ka buɗo ko rufe na bayanai, asalin na’urar dake sarrafa waɗannan bayanai ko umarni ko hani da kake ba wayar, a jikin wannan na’ura yake.

A taƙaice dai, wannan ɓangare na SoC wata ƙaramar kwamfuta ce da aka ɗora akan injin wayar salular zamani.  SoC ya ƙunshi manyan na’urori ne guda bakwai, waɗanda su ne ke gudanar da dukkan abin da ya shafi ma’amala da wayar salula.  Saboda mahimmancinsu da kuma tagomashin da suke ɗauke dashi ne yasa ake kiran wannan haɗaka na na’urori da suna: “System on Chip”.  Kalmar “Chip” na nufin wani nau’i ne na na’ura da aka ƙirƙirsa daga sinadarin Silicon, ɗaya daga cikin sinadaran da Allah Ya tanada a ƙarƙashin ƙasa, mai kama da ƙarfe, amma nau’i ne na dutse daga cikin duwatsun ƙarƙashin ƙasa.  Daga cikin abin dake keɓance shi da sauran duwatsu shi ne, yana iya ɗaukan sinadaran lantarki a cikinsa, tare da taskance shi don sadar dashi ga duk abin da aka alaƙanta shi dashi.  Idan mai karatu na son ganin misalin “Chip” a aikace cikin sauƙi, ya ciro katin SIM ɗin wayarsa ta salula, zai ga yaɓe mai launin zinare yana ƙyalli.  Wannan yaɓen ne ke taskance dukkan abin dake gudanuwa tsakanin wayarka ta salula da cibiyar sadarwar kamfanin wayarka (Mobile Switching Center).  A taƙaice dai, wannan ɓangare na SoC shi ne babbar cibiyar sarrafa bayanai don gudanar da rayuwar wayar salula; daga farkon rayuwarta zuwa ƙarshe.

Ɓangaren SoC ya ƙunshi manyan na’urori guda bakwai ne.  Waɗannan na’urori dai su ne ke da alhalin tafiyar da sauran ɓangarorin wayar salula.  Shi yasa ma wasu masana ke cewa, cibiyar SoC ce ƙwakwalwar wayar salula.  A zamanin baya sadda kwamfuta ta bayyana, da yawa cikin masana sun ɗauka bayan ita, babu wata na’ura mai ɗauke da ban al’ajabi irinta.  Har wani shahararren masanin kwamfuta da na’urorin sadarwa, kuma babban Malamin jami’a mai suna David Eck, ya rubuta wani tafkeken littafi mai suna: “The Most Complex Machine: A Survey of Computers and Computing”.  To amma yanzu da tafiya tayi nisa, ya bayyana cewa wayoyin salula na zamani da ake ƙerawa a yanzu sun fi zama abin al’ajabi idan aka haɗa su da kwamfutocin gama-gari da muke amfani dasu yanzu.  Domin akwai wayoyin salular da ƙarfin sarrafa bayanan da suke ɗauke dashi ya fi na kwamfuta a wannan zamanin.

- Adv -

Kafin mu san dalilin da yasa wannan ɓangare na wayar salula ke zama sila wajen tsada ko arahar waya, zai dace muyi bayanin kowace na’ura da wannan cibiya ke ɗauke da ita.  Wani abin da zai ba mai karatu mamaki – kamar yadda yake gani a hoton dake wannan shafi namu – shi ne, wannan cibiya ta SoC, ƙarama ce ainun, girmanta duk bai shige faɗi da tsayin gaɓan yatsar ɗan manunin hannunka.  Na’urorin dake ɗauke cikin wannan cibiya dai su ne:

Central Processing Unit (CPU): 

Wannan ita ce na’urar sarrafa bayanan babbar manhajar wayar salula, wato Operating System kenan.  Ya Allah Android ce ko iOS.  Da zarar ka kunna wayar salularka, wannan ɓangare ne ke kwaso bayanan babbar manhajar wayar salular daga ma’adanarta (Storage) zuwa ma’adanar wucin-gadi, wato: RAM kenan, kamar yadda na bayyana mana a makonnin baya.  Na’urar CPU ce ƙwakwalwar wayar salula, kamar yadda take ƙwaƙwalwar kwamfuta.  Idan kaji an ce wa kwamfuta “Na’ura mai ƙwaƙwalwa”, to, wannan na’ura ce asalin ƙwaƙwalwar kwamfuta ko wayar salula.  Idan ka baiwa wayarka umarni ta hanyar latsa wata alama don shiga wani wuri ko fita daga wani wuri misali, wannan na’ura ce ke fahimtar abin da kake nufi, kuma ita ce ke sarrafa umarninka zuwa abin da kake so.  Haka lamarin yake ga dukkan wata manhaja da za ka yi ta’ammali da ita akan wayarka.  Wannan na’ura ta CPU ce ke sarrafa umarninka baka damar gani ko ta’ammali da abin da kake buƙata.

Graphics Processing Unit (GPU): 

Wannan na’ura ita ce ke lura da sarrafa bayanan da suka shafi na’ukan manhajoji masu nauyi wajen sarrafawa, kamar manhajojin wasan wayar salula (Mobile Games), ko sarrafa bayanai masu ɗimbin yawa cikin ƙanƙanin lokaci.  Ita ce na’urar dake taimaka wa wayar salula karɓan umarnin masu amfani da manhajar wasa; ya Allah na gudun mota ne, ko wasan ƙwallo, ko na yaƙi, ba tare da wayar tana seɓi ko zafi ba saboda yunƙurin sarrafa bayanai masu ɗimbin yawa cikin ƙanƙanin lokaci.  Samuwar wannan na’ura akan injin wayar salula na cikin dalilan dake sa a samu wayoyin salular da suka fi kwamfuta ƙwari wajen sarrafa bayanai masu ɗimbin yawa cikin lokaci taƙaitacce.  Galibin kwamfutoci, idan ba kwamfutoci na musamman da ake amfani dasu a ɗakuna da cibiyoyin binciken kimiyyar likitanci ko sararin samaniya ta amfani da sabuwar ƙirƙirarriyar fasaha ba, wato Artificial Intelligence (AI), duk sauran na zuwa ne da na’urar CPU kaɗai.  Idan kana buƙata ne sai ka saya daban ka ɗora wa kwamfutar.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.