Bayani Kan Ɓangarorin Wayar Salula da Dalilan Tsada ko Araharta (10)

Nau'uka Na'urar Senso

Wannan tsari na daidaita hasken sikirin ɗin wayar salula na zamani kai tsaye – wato da kanta – ba tare da mai wayar ne yayi ba, shi ake kira: Automatic light adjustment.  Wasu kamfanonin ƙera wayar salula kuma suna kiranshi da sunaye kala-kala. – Jaridar AMINIYA, Jumma’a, 6 ga watan Oktoba, 2023.

118

Na’urar “Gyroscope”

Wannan na’ura mai suna Gyroscope ita ma ana gina ta ne a cikin wayar salula don taimaka wa manhajojin wayar salula masu alaƙa da yanayin tsayuwa ko kwanciyarta damar aiwatar da ayyukanta.  Tana aiki ne ta haɗin gwiwa da na’urar Accelerometer da bayaninta ya gabata a makon jiya.  Galibin manhajojin dake amfani da wannan na’ura a wayar salula su ne manhajojin wasan waya, wato: “Mobile Games App”, waɗanda ke buƙatar a riƙa kwantar da wayar ta gefen hagu ko ta dama kaɗan, ba wai kwantarwa cikakke ba, a yayin da ake buga wasa – musamman wasannin dake da alaƙa da tseren motoci, ko ababen hawa, kamar jirage da wasu dabbobi.  A taƙaice dai, duk wata manhajar waya da idan ana amfani da ita za ta buƙaci a riƙa kwantar da wayar a kaikaice, ko a tsayar da ita a kaikaice (wato “Tilting” kenan a harshen Turanci), to, tana amfani ne da wannan na’ura mai suna Gyroscope.  Kuma kamar yadda na sanar, tana aiki ne da na’urar Accelerometer wajen aiwatar da aikinta, kasancewar tsarin aikinsu iri ɗaya ne.

Na’urar “Digital Compass”

Asalin kalmar “Compass” tana ishara ne ga na’urar da ake amfani da ita wajen gano bigire – gabas ne, ko yamma, ko kudu, ko arewa.  Ma’ana, ana amfani da ita wajen gano bigiren wurare a wannan duniya ta mu.  Na’ura ce da asali ake ƙerawa ta amfani da fasahar ƙere-ƙere a ƙarnonin baya.  Da bayyanar wayar salula da sauran na’urorin sadarwa na zamani, sai aka ƙera tauraron ɗan adam nau’uka daban-daban aka cilla su zuwa sararin samaniya don lakato bayanan yanayi, ko watsa labaran rediyo ko na talabijin, ko kuma sinsino bayanai masu alaƙa da tsarin rayuwa a wasu duniyoyin.  Waɗannan taurari dai ana amfani da siginar rediyon sadarwa ne wajen sarrafa su a nan ƙasa.

Da aka samu ƙarin ci gaba sai aka samar da na’urar “Compass” irin wancan ta da, amma a yanayin na’ura dake maƙale a cikin wayar salula.  Kuma da wannan na’ura ake amfani wajen aiwatar da sadarwa da taurarin ɗan adam dake warwatse a sararin samaniya, don gano bigire.  A taƙaicen taƙaitawa dai, na’urar Digital Compass ana amfani ne da ita wajen gano bigiren wani gari, ko wata na’ura, ko wani mutum dake wani mahalli ko bigire a wannan duniya, ta amfani da manhajar gano bigire.

Bayan manhajar gano bigire na Google (Google Maps) dake amfani da wannan manhaja wajen gano bigire ko kusurwa, akwai manhajojin tantance alƙibla dake amfani da ita har wa yau.  A taƙaice dai, duk wata manhaja dake da alaƙa da gano inda wani abu yake, ko wani gari ko birni ko mahalli, a wannan duniya, to, wannan na’ura ta Digital Compass ce ke bata damar aiwatar da aikinta a jikin wayar salula.

- Adv -

Na’urar “Ambient Light”

Wannan na’ura ita kuma aikinta shi ne taimaka wa wayar salula tantance yanayin haske ko rashinsa a inda aka kunna wayar ana amfani da ita.  Kamar yadda a baya muka karanta a maƙalolin dake mana bayani kan haske da nau’ukansa, asalin haske dake samuwa a wannan duniya, Ya Allah na rana ne ko na wata, shi ake kira: Ambient Light – asalin haske kenan.  Shi ne hasken da ba ka iya gani dashi a inda babu wani haske da ɗan adam ya tanada.  Idan da safe ne, hasken da kake gani kafin fitowar rana, duk wannan nau’in hasken ne.  Haka idan yamma ta yi, rana ta sunkuya tana shirin faɗuwa, hasken da kake ganin gari dashi, duk ana kiransa Ambient light.

A ƙa’idar da aka gina wayar salula ta zamani, idan ka kunna ta, nan take wannan na’ura ce ke sinsino mata yanayin mahallin da ake amfani da ita.  Idan akwai haske sosai, sai fuskar wayar, wato Sikirin kenan, ya ƙara haske don taimaka wa mai amfani da wayar ganin abin dake shafin da yake ta’ammali dashi.  Idan kuma inda aka kunna wayar ake amfani da ita babu haske, ko kuma hasken bai da ƙarfi, to, nan take sai wannan na’ura ta rage kaifin hasken dake kan sikirin ɗin wayar, nan take.

Wannan tsari na daidaita hasken sikirin ɗin wayar salula na zamani kai tsaye – wato da kanta – ba tare da mai wayar ne yayi ba, shi ake kira: Automatic light adjustment.  Wasu kamfanonin ƙera wayar salula kuma suna kiranshi da sunaye kala-kala.  Misali, kamfanin Samsung na kiransa da suna: Adaptive Brightness.  Wato nau’in hasken dake dacewa da yanayin da wayar take.  Idan ka cire wayarka daga wannan tsari, to, hasken sikirin ɗinta na daidai ne da yadda ka ƙara ko rage masa kaifi.  Wayar ba za ta iya amfani da wannan na’ura na Ambient light don daidaita shi ba.  Idan kaje ɓangaren Display a cikin Settings, za ka ci karo da wannan tsari dake daidaita yanayin hasken waya ta la’akari da hasken dake mahallin da wayar take.

Proximity Sensor

Sai na’ura ta ƙarshe, ko ince nau’in na’ura ta ƙarshe wacce ake kira: Proximity Sensor.  Wannan na’ura aikinta shi ne, a duk sadda ka kusanto da wayar zuwa kunnenta sadda kake son amsa kira, nan take za ta alamta wa wayar cewa amsa waya za ka yi, ita kuma manhajar sadar da kira dake wayarka sai ta kunne sikirin ɗin wayar nan take, don kada wajen kara wayar a kunnenka ka katse kiran baka sani ba.  Aikin wannan na’ura kenan, wato kulle fuskar waya yayin amsa kira don hana katsewar kira.  Nan gaba akwai tabbacin samun ƙarin wasu manhajojin da za su riƙa amfani da wannan na’ura wajen aiwatar da wasu ayyuka a wayar salula.

A taƙaice dai, samuwar waɗannan na’urori dake taimaka wa wayar aiwatar da wasu ayyuka na musamman na cikin dalilan dake sa wayar salula tsada, da kuma bambanta farashinta da sauran wayoyin da suke da ƙarancin waɗannan na’urori.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.