Ɓangarorin Wayar Salula da Dalilan Tsada ko Araharta (18)

Kamfanin Huawei

Asalin kalmar “Huawei” kalma ce ta yaren mandarin, wato harshen mutanen ƙasar Sin kenan.  Abin da kalmar take nufi shi ne: “kyautata fata”, ko “cin nasara a rayuwa”.  Wannan ma’ana kuwa na bayyana ne a aikace a dukkan na’urorin da kamfanin ke samarwa. – Jaridar AMINIYA, Jumma’a, 1 ga watan Disamba, 2023.

98

Wayoyin Huawei

Kamfanin Huawei ɗaya ne daga cikin shahararru kuma manyan kamfanonin ƙera wayoyin salula a duniya, musamman a gabashin Asiya.  Asalin kamfanin ƙasar Sin ne.  Bayan wayoyin salula, kamfanin Huawei na ƙera na’urorin sadarwar Intanet, irin su Wi-Fi Router, wato na’urar dake isarwa da kuma daidaita siginar Intanet tsakanin na’urorin sadarwa.  Sannan yana samar da wasu na’urorin ma daban da suka danganci fannin sadarwa a duniya.  Kafin shekarar 2019, kamfanin Huawei ya yi wa sauran kamfanonin ƙera wayar salula na duniya fintinkau wajen yawan wayoyin da yake samarwa a shekara, da yawan wayoyin sa yake sayarwa a kowace shekara.  Sai da aka wayi hatta a ƙasar Amurka, inda kamfanin Apple yake taƙama da kasuwarsa, sai da wayoyin kamfanin Huawei suka fi na kowane kamfani samun kasuwa da riba a duk shekara.

Asalin kalmar “Huawei” kalma ce ta yaren mandarin, wato harshen mutanen ƙasar Sin kenan.  Abin da kalmar take nufi shi ne: “kyautata fata”, ko “cin nasara a rayuwa”.  Wannan ma’ana kuwa na bayyana ne a aikace a dukkan na’urorin da kamfanin ke samarwa.  Domin idan ka keɓance wayoyin kamfanin Apple, wato iPhone, da wahala ka samu wayoyin salula masu inganci gini, da kyaun siffa, da nagartar sadarwa a tsakanin sauran kamfanonin ƙera wayoyin salula a duniya.  Ba don takunkumin da ƙasar Amurka ta sanya wa kamfanonin sadarwa na ƙasar Sin ta hanyar hana kamfanonin ƙasar Amurka sayar wa kamfanonin ƙasar Sin wasu ɓangarori da fasahohi masu alaƙa da sadarwa ba, da tuni ba ka jin sautin wata wayar salula a duniya wajen nagarta da inganci face na kamfanin Huawei.

Ta ɓangaren sauki ko tsadar farashi kuma, wayoyin kamfanin Huawei na kama da sauran kamfanoni ne – irin su Samsung da sauransu – a ɓangare ɗaya.  A ɗaya ɓangaren kuma wayoyin kamfanin Huawei na kama da na kamfanin Apple ne, wato iPhones.  Abin da wannan zance ke nufi kuwa shi ne, wayoyin kamfanin Huawei sun kasu kashi uku ne.  Akwai masu tsantsar rahusa, wato masu araha kenan.  Waɗannan su ne nau’ukan wayoyin da masana kan musu laƙabi da “Budget Phones”.  Wato an ƙera su ne don masu ƙaramin ƙarfi, kamar yadda bayani ya gabata makonni uku da suka shige.

Sai ɓangare na biyu, wato nau’ukan wayoyin salula masu matsakaitan farashi.  Su kuma sun ɗara na farko wajen farashi, sannan sun ɗara su wajen siffofi da nagarta.  Bayani ya gabata a baya har kan siffofin waɗannan nau’ukan wayoyin salula, waɗanda masana kan kira su da suna: “Mid-range Phones”.

- Adv -

Sai ɓangare ko kashi na ƙarshe da ake kira da suna: “Flagship Phones”.  Waɗannan su ne wayoyin masu hannu da shuni a al’adance, ko duk wani mai sha’awa kuma yake da kuɗi da ikon sayansu.  Su ne ƙololuwa wajen mizani, da nagarta, da ingancin na’ura da hanyoyin sadarwa.  Don haka su suka fi sauran ɓangarorin tsada da tagomashi.

Bayan wannan bayani da ya gabata, a ɗaya ɓangaren kuma wayoyin kamfanin Huawei na kama da nau’ukan wayoyin kamfanin Apple wajen inganci da tagomashi da nagartar na’ura, tare da kyakkyawar siffa na zahiri.  Na sanar a farko cewa ba don takunkumin da gwamnatin Amurka ƙarƙashin shugabanin tsohon Shugaga Trump ba a shekarar 2019, da tuni kamfanin Huawei ya shallake sauran kamfanonin wayar salula a duniya wajen yawan wayoyin da ake ƙerawa a shekara, da yawan wayoyin da ake sayarwa a duk shekara, saboda nagarta da inganci da kuma kyaun siffa da wayoyinsa ke ɗauke dasu.

Alal haƙiƙa wayoyin Huawei suna da tsada.  Shi yasa, bayan rabe-raben da kamfanin yayi na darajar wayoyinsa – daga na masu ƙaramin ƙarfi zuwa sama – a ɗaya ɓangaren kuma in ka dubi, ta la’akari da mu dake ƙasashe masu tasowa, farashinsu na da tsada.  Tabbas a baya ya ƙera wayoyi masu matsakaitan farashi kam, irin su Huawei Y9 (2019), wacce na taɓa amfani da ita na tsawon shekaru 3, Huawei Y9 Prime misali.  Amma daga baya wayoyin Huawei sun kere Kundila.  Misali, galibin wayoyin da kamfanin ya ƙera daga shekara ta 2021 zuwa yanzu, da wahala ka samu wacce take ƙasa da naira dubu 100 a ƙimar kuɗin kasarmu. Galibi daga naira dubu 150 ne zuwa sama.  Sabuwar wayarsa da ya fitar cikin watan Satumba da ya gabata mai suna Huawei Mate 60, da sauran zubinta irin su Huawei Mate 60 Pro, da kuma Huawei Mate 60 Pro+ sun yi matuƙar ƙayatar da duniya, a ɗaya ɓangaren kuma bayyanar waɗannan nau’ukan wayoyi, ta la’akari da irin fasahar sarrafa bayanai (Processor) da kamfanin yayi amfani dasu, sun tsorata hukumar ƙasar Amurka da ‘yan korenta. Dalilin hakan na tafe nan da makonni biyu in Allah Ya so.

A taƙaice dai, wannan sabuwar waya na kamfanin Huawei tana kunnen doki ne da iPhone 15, wadda ita ce kankat a jerin wayoyin salula na zamani a yau – kamar yadda a al’adance ake ɗauka – kuma mafi tsada.  Huawei Mate 60 Pro bata tsaya a nan ba kaɗai, wayar tana ɗauke ne da tsarin sadarwa na tauraron ɗan adam, wato Satellite Network, wanda zai baka damar iya aiwatar da kira ko karɓan kira a wurin da babu siginar sadarwar kamfanin wayarka.  Ko a cikin kogo ne, ko saman tsauni, da cikin rami mafi zurfi, duk kana iya samun siginar sadarwa.

A ƙarshe dai, wannan shi ne tsarin kamfanin Huawei dangane da abin da ya shafi tsada ko rahusan wayoyin da yake ƙerawa. A makon gobe in Allah Ya so za mu ƙarƙare wannan jerangiyar bayanai da muka faro sama da watanni huɗu da suka gabata.  Bayan nan za mu juya da bayani kan fanni da fasahar Artificial Intelligence, wato “AI” kenan.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.