Ɓangarorin Wayar Salula da Dalilan Tsada ko Araharta (13)

Nau'ukan Kyamarar Wayar Salula

Duk kyamarar da take da tabarau (Lens) mai cin dogon zango, ita ake kira Telephoto Camera.  – Jaridar AMINIYA ta ranar Jumma’a, 27 ga watan Oktoba, 2023.

223

Nau’ukan Kyamarar Wayar Salula

Na’urar ɗaukan hoto na wayar salula na karkasuwa ne ta hanyoyi daban-daban.  Hanyar farko ita ce ta ɓangaren mahalli.  Dangane da mahallin samuwar kyamara a wayar salula, kyamara ta kasu kashi biyu ne.  Akwai asalin kyamara wacce ita ce a bayan wayar salula.  Wannan ita ake kira Main Camera, ko kuma Rear Camera.  Wato kyamara ta asali, ko kuma kyamarar baya.  Ita ce ke ɗaukan hoton abin da ke gabanka kai tsaye.  Kuma tana ɗauke ne da hanyar ɗaukan hoto da na bidiyo.  Ita ce asalin kyamara a wayar salula, kafin ci gaba yazo a samar da mai biye mata.

Sai nau’in kyamara ta biyu ta la’akari da mahalli, wato kyamarar dake gaba, wacce ake kira Front Camera, ko kuma Selfie Camera.  Ita wannan kyamara tana ɗaukan abin dake fuskarka ne, ko bayanka, idan ka karkatar da ita.  Ita ma tana ɗaukan hoto kamar yadda take ɗaukan bidiyo, kai tsaye.  Sai dai a galibin lokuta, kyamara ta asali, wato Main Camera ko Rear Camera, ta fi kyamarar gaba inganci, da ƙarfin ƙudura wajen sinsino haske da sarrafa shi.  Hatta mizaninta ya fi na kyamarar gaba, nesa ba kusa ba. Galibin masu yaɗa hotunan bidiyo a kafafen sada zumunta irin su Tiktok, da Instagram, da Facebook Reel, duk suna amfani ne da kyamarar gaba na wayar salula.

Sai nau’in kyamara ta la’akari da aikinta.  Waɗannan nau’uka ne ta la’akari da aiki, kuma abin da hakan ke nufi shi ne, kyamarori ne ake ginawa a bayan wayar salula.  Wata na zuwa da guda uku.  Wata guda biyu.  Wata kuma kaga ƙwaya ɗaya kawai tazo dashi.  Ko ma dai mene ne, duk wayar da ka ganta da kyamara guda uku a bayanta, to, kowanne aikinta daban.  Ga bayanin kowannensu nan:

Normal Camera

Wannan ita ce kyamara ta asali dai, har wa yau.  Ma’ana, mai ɗaukan hoto da bidiyo a yadda aka san kyamara na ɗauka tun farkon bayyanarta.  Tana gudanar da aikinta ne na janyo haske, da shigar dashi cikin tabarau, tare da sarrafa shi don fitar da surar abin da aka ce ta ɗauka.  Tana iya zama kyamarar baya (Rear Camera), ko kuma kyamarar gaba (Selfie Camera).

Ultrawide Camera

- Adv -

Wannan nau’in kyamara aikinta shi ne, bayan aikin ɗarsano haske da sarrafa shi don samar da hoto, tana iya faɗaɗa mahallin ɗaukan hoton, fiye da kusurwa 90, har zuwa kusurwa 140 ma, musamman a wayoyi masu tsada.  Abin da hakan ke nufi shi ne, kana iya ɗaukan hoton abubuwa masu yawa a mahalli guda, ba tare da ta yanke maka wasu ba.  Abin da kyamara ta asali ba ta iya yi.

Telephoto Camera

Ita kuma wannan, tana iya ɗaukan hoton abubuwa masu nisa ne daga inda take.  Za ta iya janyo su kusa duk tazararsu, ba tare da an samu tauwayar ingancin hoton ba.  In mai karatu bai mance ba, a baya na tabbatar da cewa, ingancin hoto na tabbata ne ta la’akari da daidaiton haske a inda yake, da kuma nufatar abin kai tsaye.  Nace wannan sharaɗi na biyu shi ne natsuwar ƙwayar ido – idan ɗan adam ne – wajen ɗaukan surar abin da ake son samun hotonsa.  A harshen kimiyyar ɗaukan hoto kuma ana kiransa da suna Focus.  Wannan ɗabi’a na “natsuwa” da “nufin” abin da ake son ɗaukan surarsa wajen kallo, an gina shi cikin kyamarar ɗaukan hoto.  Duk abin da aka nuface shi da kyau don ɗaukan surarsa, ana samun surar yadda ake so.  Amma idan a yashe aka kalle shi, ko an tuna an taɓa ganinsa, surarsa ba za ta zama raurau a cikin ƙwaƙwalwa ba.

To a ɓangaren ɗaukan hoto ma haka lamarin yake.  Duk kyamarar da take da tabarau (Lens) mai cin dogon zango, ita ake kira Telephoto Camera.  Tabarau ɗin kuma a kira shi da suna Telephoto Lens.  Na Wayar salula ba a iya canzawa; yadda tazo dashi haka za ka haƙura.  Amma na kyamarorin zamani – DSLR –  ana iya canzawa, musamman irin wanda ya dace da nau’in kyamarar, a bisa shawarar kamfanin da ya ƙera ta.

A taƙaice dai, wannan kyamara mai ɗauke da tabarau mai cin dogon zango, da ita ne ake ɗaukan hotunan taurari ka gansu raurau.  A taƙaice duk wani abu mai nisan gaske, da wannan kyamarar ake amfani wajen ɗaukansa.  Don ita ce ke iya hango shi duk tazarar dake tsakaninsa da ita, sannan ta ɗauko shi ba tare da an rasa ingancinsa ba.

Macro Camera

Ita kuma Macro Camera da ita ake ɗaukan hotunan abubuwan dake kusa da kai, amma saboda ƙanƙantarsu, ba za ka iya samunsu yadda kake so ba.  Ita an gina ta ne da na’urar hango ƙananan abubuwa, irin wacce ake amfani da ita a ɗakunan binciken kimiyya musamman wajen gano ƙwayoyin cututtukan da idanu ba sa iya gani.  Sai dai saɓanin sauran kyamarori dake iya hango abubuwa daga nesa har ma su jawo su kusa, iya ƙarfin yadda aka gina tabarau ɗinsu, ita wannan nau’in kyamarar ba ka iya hango abin dake nesa sai ka matso kusa dashi ainu.  Daga sadda ka kunna ta ma, duk abin da ke nesa za ka ganshi biji-biji ne, kamar hazo ya rufe shi.  Da zarar ka zo kusa dashi ainun, nan take sai idon tabaranta ya buɗe garau, sai kaga abubuwa raɗau-raɗau.

Waɗannan su ne nau’ukan kyamarar wayar salula a taƙaice.  A mako mai zuwa za mu ƙarƙare bayani da siffofin kyamarar wayar salula.  Aci gaba da kasancewa tare damu har kullum.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.