Ɓangarorin Wayar Salula da Dalilan Tsada ko Araharta (11)

Kyamarar Wayar Salula

Za mu dubi ɓangarorin kyamarar wayar salula, da nau’ukan kyamarar wayar salula, da siffofin kyamarar wayar salula, da kuma wayoyin salular da suka yi wa sauran fintinkau wajen kyaun kyamara masu ƙayatarwa.  – Jaridar AMINIYA ta Jumma’a, 13 ga watan Oktoba, 2023.

85

Kyamarar Wayar Salula (Mobile Camera)

Daga cikin dalilai dake bambance wayoyin salula wajen tsada ko rahusa, akwai nau’in na’urar ɗaukan hoto, wato kyamarar da wayar ke ɗauke dashi.  Alal haƙiƙa wannan na cikin manyan dalilai da suka sabbaba haɓaka da yaɗuwa da kuma shaharar wayar salula a duniya baki ɗaya.  Nau’in kyamarar wayar salula har wa yau yasa hatta kyamarorin ɗaukan hoto da bidiyo na zamani da ake kira Digital Single Lens Reflex Cameras ko kace DSLR Cameras a gajarce, ya ƙwace musu kasuwa a duniya.  Ba su kaɗai ba, wannan na’ura ce tasa kusan gama-garin mutane, waɗanda a baya basu taɓa sanin yadda ake ɗaukan hoto ba, sun wayi gari shahararrun masu ɗaukan hoto – mai motsi da daskararre.

Yadda wannan na’ura ta ɗaukan hoto da bidiyo, wato kyamara, tasa wayar salula tayi wa sauran na’urorin ɗaukan hoto hatta na zamani fintinkau, haka wannan na’ura ke sa a samu bambancin farashi tsakanin wayar salula da wata wayar salular.  Daga wannan mako zuwa mai zuwa in Allah Ya so, za mu yi bayani filla-filla kuma dalla-dalla kan wannan na’ura ta kyamara.  Domin ta haka ne kaɗai mai karatu zai fahimci dalilan dake sa bambancin farashi tsakanin wayoyin salula.  Za mu dubi ɓangarorin kyamarar wayar salula, da nau’ukan kyamarar wayar salula, da siffofin kyamarar wayar salula, da kuma wayoyin salular da suka yi wa sauran fintinkau wajen kyaun kyamara masu ƙayatarwa.  Amma kafin nan, bari mu fahimci yadda ɗan adam ke amfani da idonsa wajen ɗaukan hoto tukun.

Ɗaukan Hoto a Aikace

Yadda kyamarar wayar salula ko na’urar kyamara ta musamman ke ɗaukan hoto, abu ne mai ban al’ajabi.  Sai dai abin da ya fi shi zama abin al’ajabi shi ne halittar da aka kwaikwaya wajen ƙera na’urar kyamara.  Wannan halitta kuwa ita ce halittar idon ɗan adam ko ta dabba.  A taƙaice dai, halittar ido.  Idon ɗan adam na amfani ne da haske wajen taskance abin da ya hango kuma ya mayar da hankali wajen kallonsa.  Hoton duk abin da ka kalla na zama a ƙwaƙwalwarka ne ta amfani da wasu matakai.

- Adv -

Matakin farko shi ne aiken ido don ya kalli abin.  Wannan kuma yana faruwa ne idan ka fuskanci abin, alhalin idanunka na mai kallonshi.  Sai mataki na biyu, wato  riskar abin a bisa yanayin da yake.  Wannan kuma na faruwa ne ta hanyar hasken dake mahallin da abin yake, wanda ke shigowa cikin ƙwayar idon ɗan adam.  Da zarar hasken dake ɗauke da siffar abin da aka kalla ya shige cikin ƙwayar idanu, nan take sai wata na’ura dake cikin ƙwaƙwalwa ta sarrafa waɗannan bayanai masu ɗauke da surar abin, zuwa haƙiƙanin yadda yake, iya gwargwadon ƙarfin hasken dake mahalli ko rauninsa.

Mataki na uku kuma shi ne daidaiton ƙwayar ido a lokacin da ake sawwara abin da ake kallo.  Wannan kuma na samuwa ne ta hanyar nufi ko niyyar riskar abin a yadda yake ba tare da tangarɗa ba.  Idan mai kallon abin bai mayar da hankalinsa kan abin ba da niyyar riskar haƙiƙanin surarsa, ƙwaƙwalwarsa za ta haddace surar abin amma na taƙaitaccen lokaci, kuma ba da kyakkyawar sura ba. Tunda ba  manufar mai kallo bane tun asali.

A warware cikin sauƙi, matakin farko shi ake kira: Composition, a ilimin ɗaukan hoto ko bidiyo na zamani.  Wato killacewa da kuma haddade abin da ake son kallo ko ɗauka, tare da keɓance abin da ba a son ya shiga ciki.  Mataki na biyu kuma shi ne la’akari da yawa ko kaifin haske a mahallin da abin yake.  Domin ƙwayar idon ɗan adam na da iya gwargwadon hasken da yake buƙata wajen ɗaukan hoton kowane abu ne ya gani.  Idon ne kuma ke haddade iya yawan hasken dake shiga cikinsa, ta amfani da kafar shigan hasken.  Ƙwayar idon shi ake kira: Lens; wato kamar tabarau ɗin idon ɗan adam kenan, kuma a cikinsa ne kafar da haske ke shiga take.  Sannan yana ɗauke da wata na’ura mai iya jawo haske kai tsaye don shiga wannan kafa, wacce ake kira: Lens Sensor.   Ita kuma kafar shigan hasken ana mata laƙabi da: Aperture.  Sannan akwai iya gwargwadon lokacin da haske ke ɗauka kafin shiga wannan kafa.  Kadadar lokacin hakan shi ake kira: Shutter speed.  Iya yawan hasken da ake buƙata ya shiga wajen kuma, shi ake kira ISO.  Kalmar ISO jerin haruffa ne ko laƙabi ne, ba suna bane cikakke.

Mataki na uku kuma da muka ce ya ƙunshi daidaiton ƙwayar ido yayin da yake sawwara abin da yake kallo, shi ake kira: Focus.  Wannan daidaito yana samo asali ne daga ƙwaƙwalwa ko zuciya.  Duk abin da ɗan adam ya mayar da hankalinsa da nufinsa wajen kallonshi sosai, dole ƙwaƙwalwarsa za ta taskance abin raɗau a cikinta.  To haka ma ɗaukan hoto yake.  Kuma ɓangaren dake sarrafa bayanan da ido ya ɗebo don samar da hoto ko surar abin da ido ya kalla, shi ake kira: Image Processor.  Wanda Allah Ya sanya wa ɗan adam yana tsakanin ƙwaƙwalwarsa ne da ƙwayar idonsa.

Da wannan ne ɗan adam zai fahimci irin tsabar kimiyyar da aka zuba wajen ƙera kyamarar wayar salula – ta la’akari da ƙanƙantarta – fiye da sauran kyamara masu zaman kansu na zamani, wato: DSLR Cameras.  Mako mai zuwa za mu shiga bayani kan manyan ɓangarorin kyamarar wayar salula.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.