Yawaitar Motoci Masu Makamashin Lantarki a Duniya: Ina Muka Dosa? (2)

Kasar Sin ta ba da sanarwar daina amfani da motoci masu amfani da makamashin man fetur da dizil a kasarta zuwa shekarar 2040.  A makon jiya mun fara yin nazari kan sakon dake dunkule cikin wannan sanarwa nata, da kasashen da suka yi wanann kuduri kanfinta, da sakamakon hakan ga kudaden shigarmu a Najeriya, sannan a karshe muji bayani kan motoci masu amfani da makamashin lantarki da yanayinsu.  Ga kashi na biyu cikin wannan nazari namu nan.  A sha karatu lafiya.

Karin Bayani...

Zuwa Sararin Samaniya: Abu Mai Yiwuwa da Mara Yiwuwa (1)

Edward Teller masani ne a fannin kimiyyar sararin samaniya da kimiyyar sinadarai (Physics and Chemistry), kuma ya samar da ka’idojin bincike da kere-keren kimiyya a duniya da dama.  Mutum ne mai wuyan sha’ani a lokacin rayuwarsa, kuma ya shahara wajen rajin kawo sauyin kere-kere a fannin kimiyyar sararin samaniya, inda ra’ayoyinsa suka bambanta matuka da ra’ayoyin abokan aikinsa a fannin ilimi.  Duk da haka, ya yi hasashen yiwuwan faruwa ko rashin yiwuwan faruwar abubuwa da yawa a fannin kimiyya; wasu sun tabbata haka, kamar yadda mai karatu zai gani, wasu kuma basu tabbata ko ba, ana zaman jiransu. Wasu kuma, tarihi ya karyata shi a kansu.  A yau za mu karantu wasu daga cikin hasashensa, wanda daya daga cikin masu karatu, mai kwazo da kokarin bincike, wato MALAM SADIK TUKUR GWARZO (sadiqtukurgwarzo@gmail.com) ya kawo mana.  A sha karatu lafiya.

Karin Bayani...

Sakonnin Masu Karatu (2017) (3)

Assalamu alaikum Baban Sadik, Allah ya kara basira amin.   Don Allah ka turo mini kasidarka kan tsibirin “Bamuda Triangle” ta imel dina dake: ibrahimali056@naij.com. Daga Yahya (Abban Humairah), Gombe: 08035767045   Wa alaikumus salam, barka ka dai Malam Yahya.  Ina godiya da addu’o’inku.  Ka duba akwatin Imel dinka, na cillo maka kasidar, kamar yadda ka…

Karin Bayani...