Sakonnin Masu Karatu (2011) (1)

A yau kuma, kamar yadda muka saba lokaci zuwa lokaci, ga mu dauke da sakonninku da kuka aiko to tes.  Galibin sakonnin da nake samu ta Imel nan take nake amsa su, musamman idan ba suna dauke ne da wasu bukatu da ke bukatar doguwar bincike ba.  Bayan haka, idan sako ya sha maimaituwa ba na amsa shi.  Don haka sai dai a yi hakuri. Idan muka ce za mu rika maimata tambayoyi, musamman ma wadanda suka sha maimaituwa a wannan shafi, a gaskiya ba za mu ci gaba ba.  Da fatan za a yi hakuri da wannan ka’ida.  A yanzu dai ga abin da ya sawwaka.

Karin Bayani...

Fasahar Sadarwa ta Infara-Red

A yau mun dawo don ci gaba da bayani kan tsarin sadarwa ta wayar iska, inda za mu yi bayani kan wani tsari, makamancin tsarin da ya gabata na Bluetooth.  Wannan tsari shi ne tsarin sadarwa ta amfani da fasahar sadarwa ta Infra-red.  Kamar tsarin sadarwa ta Bluetooth, Infra-red ya kunshi tsarin sadarwa ne daga wani kayan fasahar sadarwa zuwa wani, amma a iya tazarar da bai kai na Bluetooth ba.  A yau za mu ji tarihin wannan tsari ; yaushe ya samu, me da me ake yi dashi, yaya tsarin ke kasancewa, wasu irin kayayyakin fasahar sadarwa ne ke amfani dashi, kuma me ye alakar da ke tsakanin fasahar sadarwa ta Bluetooth, da na Infra-red ?  Idan mai karatu na tare damu, duk zai samu wadannan bayanai cikin yardar Ubangiji.  A biyo mu.

Karin Bayani...