Wadanda suka saba karanta wannan shafi tun farkon farawa sun san cewa a duk karshen zango, mukan zauna don tattaunawa da juna, da kuma yin waiwaye, abin da Malam Bahaushe ke kira “Adon tafiya.” A yanzu shekarun wannan shafi namu biyar kenan da watanni shida cif-cif. Kuma wannan shi ne zama na biyar da za mu yi, don yin bitar darussan da muka yi ta kwasa a baya. Ga wadanda basu san wannan tsari da shafin ke gudanuwa a kai ba, shafin Kimiyya da Kere-kere ya samo asali ne cikin watan Oktoba na shekarar 2006; farkon taken shafin shi ne: Kimiyya da Fasaha. Mun kuma yi waiwaye karo na daya, da na biyu, da na uku ne a tsakanin shekarar 2006 zuwa 2008. Zama na karshe da muka yi, wanda shi ne waiwaye na hudu, ya zo ne cikin watan Satumba na shekarar 2008, daidai lokacin da shafin ya cika shekaru biyu kenan. Ga shi mun sake dawowa a yau don yin nazari kan kasidun baya, a karo na biyar, kamar yadda masu karatu za su gani daga taken kasidar.