![Kasashe Masu Karfin Nukiliya a Duniya (2)](https://babansadik.com/wp-content/uploads/2017/03/nukiliya-6.png)
Kasashe Masu Karfin Nukiliya a Duniya (2)
Ci gaba da bayani kan kasashe masu karfin nukiliya a duniya. A sha karatu lafiya.
Makaloli a fannin kimiyya da fasaha!
Ci gaba da bayani kan kasashe masu karfin nukiliya a duniya. A sha karatu lafiya.
Kasidarmu ta wannan mako ta yi tsokaci ne kan dokar hana yaduwar makamin nukiliya a duniya. A sha karatu lafiya.
Makamin nukiliya yana da hadari matuka, saboda irin sinadaran da yake dauke dasu masu guba. A wannan mako mun gudanar da bincike ne kan tasirin wadannan sinadarai masu guba.
A wannan mako mun dubi asali da samuwar makamin nukiliya ne a duniya. A sha karatu lafiya.
Daga cikin abin da kasashen duniya ke rige-rige wajen mallaka akwai makamin nukiliya. Daga wannan mako za mu fara gudanar da bincike don kosar da masu karatu kan wannan makami, a kimiyyance. Wannan shi ne kashi na daya.
Dumamar yanayi, ko “Global Warming” kamar yadda ake kira a turance, yanayi ne da halin yanzu yake game duniya. A kasashenmu nan da yawa cikin mutane basu ma san me hakan ke nufi ba, balle tasirinsa ga mahallin da muke rayuwa a ciki. Wannan yasa a wannan mako na fara kalato mana kadan daga bayani kan wannan maudu’i. A sha karatu lafiya.
Cikin watan da ya gabata ne kasar Jafan ta fuskanci wata girgizar kasa mai girma da karfin gaske, wanda kuma sanadiyyar haka nan take tekun kasar ya kama ambaliya (Tsunami). Wannan ambaliya ya kwashe gidaje da garuruwa da jama’a sama da dubu talatin – tsakanin wadanda suka mutu da wadanda aka rasa inda suke – sannan ya yi mummunar tasiri a kan cibiyoyin nukiliyar kasar, wadanda suke cikin tsibiri, daidai inda wannan lamari ya auku. A yanzu wadannan cibiyoyi na fuskantar barazanar fashewa a kowane lokaci, kuma tuni har an fara samun yaduwar mummunar tururin guba (radiation) da ke fitowa daga cikinsu. Wannan tasa muka kawo wa masu karatu bayanai kan mummunar tasirin wannan abu dake kokarin bayyana muddin ba a dauki wani mataki mai tasiri ba. Domin wannan matsala muddin ta fara yaduwa, ba kasar Jafan kadai za ta shafa ba, kusan duk duniya baki daya na cikin hadari. Saboda abu ne mai gamewa ba wai a jiki ko ruwa ko gidaje ko kasa kadai ba, har da iskar da ake shaka.
A ci gaba da bincikenmu kan makamashi, a wannan mako mun duba makamashin hasken rana ne, wato: “Solar Energy.” A sha karatu lafiya.
A bangaren kimiyyar makamashi, yau za mu fara bayani kan makamashi da ma’anarsa, da kuma nau’ukansa. A sha karatu lafiya.
A kashi na hudu kuma na karshe, munyi bayani ne akan tokar dake bulbule mahallin da tsaunin da ya kama da wuta yake. Ba wai garuruwa ko kauyukan dake wurin kadai ba, hatta sararin samaniya duk abin yana shafa.
Ga kashi na uku na binciken da muke ta faman yi kan tsaunuka masu aman wuta, wato: Volcanic Moutains.
Wannan ci gaba ne daga kasidar makon jiya, kan tsaununa masu aman wuta, musamman na kasar Ice Land. A sha karatu lafiya.