![Jirage Masu Sarrafa Kansu: Wani Sabon Salon Yaki a Duniya (1)](https://babansadik.com/wp-content/uploads/2017/03/drone-1.jpg)
Jirage Masu Sarrafa Kansu: Wani Sabon Salon Yaki a Duniya (1)
Daga cikin fasahar dake kan sharaha a fannin kere-kere yanzu a duniya akwai kirar jirage masu sarrafa kansu da ake kira: “Drones” a harshen Turanci. Daga wannan mako zamu fara bayani tarihi da samuwar wadannan nau’ukan jirage, da kuma yadda kasashen yamma ke amfani dasu cikin wani irin sabon salon yaki na zamani a duniya.