Ambaliyar Danyen Mai a Teku da Tasirinsa

A fannin “Kimiyyar Mahalli da Sinadarai”, yau za mu dubi al’amarin da ya faru a kasar Amurka, inda aka samu ambaliyar danyen mai a teku, sanadiyyar hadarin da ya faru, inda gobara ta tashi a cibiyar hako danyen mai na kamfanin Mobile dake tekun Atlantika na bangaren Amurka. Zamu dubi tarihin wannan lamari, da kuma abin da zai haddasa ga halittun dake rayuwa a wannan mahalli da abin ya faru ciki.

Karin Bayani...

Bincike Kan Bacci Da Mafarki A Mahangar Kimiyya (1)

Daga cikin dabi’un dan adam masu ban mamaki, wanda har yanzu likitocin duniya sun kasa gano hakikaninsa a kimiyyance, akwai bacci, wanda Hausawa ke kira: “Kanin mutuwa.” Daga wannan mako za mu fara gudanar da bincike na musamman kan bacci – ma’anarsa, alakarsa da mutuwa, yadda yake samuwa, ambatonsa a Kur’ani da dai sauran bayanai masu mahimmanci.

Karin Bayani...

Yadda Na’urar ATM Ke Aiki (1)

Bayan kasidar da muka gabatar a shekarun baya kan manyan matsalolin tsarin ATM a Najeriya, a halin yanzu wannan fasaha ta habbaka, kuma masu amfani da ita sun yawaita. Hakan ya dada taimakawa wajen samun karin ingancin tsari da mu’amala da na’urar ita kanta. Da yawa cikin masu karatu sun bukaci a musu bayani kan hakikanin wannan na’ura da yadda take aiki, amma a kimiyyance. Wannan shi ne abin da za mu fara gabatarwa a wannan mako. A sha karatu lafiya.

Karin Bayani...

Yadda Aka Kera Jirgin Ruwan “RMS Titanic” (1)

Shirin Fim din “Titanic” ya shahara matuka, har ta kai ga da yawa cikin mutane sun dauka kirkirarren labari ne kamar sauran mafi yawancin fina-finai. Wannan yasa naga dacewar gudanar da bincike don fahimtar damu cewa labari ne tabbatacce ba kirkirarre ba. Kalmar “Titanic” da aka baiwa shirin, sunan wani jirgin ruwa ne da aka kera mai girman gaske tsakanin shekarar 1909 zuwa 1912. A sha karatu lafiya.

Karin Bayani...