![Ma’ana da Asalin Kwayar Cutar Kwamfuta (Virus)](https://babansadik.com/wp-content/uploads/2017/03/cutar-kwamfuta-1.jpg)
Ma’ana da Asalin Kwayar Cutar Kwamfuta (Virus)
Daga wannan mako in Allah Ya yarda, za mu fara bayanai kan manyan matsalolin da ke damun kwamfuta da masu amfani da ita a wannan zamani da muke musamman. Kamar dai yadda dan Adam yake ne; yana da damuwoyi da dama da ke masa kaidi wajen tafiyar da rayuwa ingantacciya kuma cikin sauki. Haka na’urar kwamfuta take; akwai matsaloli da ke mata karan-tsaye wajen gudanar da ayyukan da aka kera ta don yin su, cikin sauki. Wadannan matsaloli suna da yawa, amma za mu dauki wadanda suka shafi lafiyarta da kwakwalwarta ne kadai, don su ne manyan matsalolin da suka fi kowanne tasiri wajen dama mata lissafi, musamman cikin wannan zamani da aka samu kwararru kan ilimin ta, birjik a duniya.