![Ɓangarorin Wayar Salula da Dalilan Tsada ko Araharta (13)](https://babansadik.com/wp-content/uploads/2023/10/Wayar-Salula-13.jpg)
Ɓangarorin Wayar Salula da Dalilan Tsada ko Araharta (13)
Duk kyamarar da take da tabarau (Lens) mai cin dogon zango, ita ake kira Telephoto Camera. – Jaridar AMINIYA ta ranar Jumma’a, 27 ga watan Oktoba, 2023.
Makaloli a fannin kimiyya da fasaha!
Duk kyamarar da take da tabarau (Lens) mai cin dogon zango, ita ake kira Telephoto Camera. – Jaridar AMINIYA ta ranar Jumma’a, 27 ga watan Oktoba, 2023.
Fahimtar waɗannan ɓangarori zai taimaka wa mai karatu musamman kan yadda ake wayar salula ko kyamarar zamani (DSLR) ke ɗaukan hotuna abubuwan dake mahalli. – Jaridar AMINIYA ta ranar Jumma’a, 20 ga watan Oktoba, 2023.
Za mu dubi ɓangarorin kyamarar wayar salula, da nau’ukan kyamarar wayar salula, da siffofin kyamarar wayar salula, da kuma wayoyin salular da suka yi wa sauran fintinkau wajen kyaun kyamara masu ƙayatarwa. – Jaridar AMINIYA ta Jumma’a, 13 ga watan Oktoba, 2023.
Wannan tsari na daidaita hasken sikirin ɗin wayar salula na zamani kai tsaye – wato da kanta – ba tare da mai wayar ne yayi ba, shi ake kira: Automatic light adjustment. Wasu kamfanonin ƙera wayar salula kuma suna kiranshi da sunaye kala-kala. – Jaridar AMINIYA, Jumma’a, 6 ga watan Oktoba, 2023.
A yau in sha Allah za mu yi bayani ne kan na’urar tantance yanayin da wayar salula ke ciki, na zahiri ko yanayin tsayuwanta ko yanayin mahallinta ko abin da take yi. – Jaridar AMINIYA, Jumma’a, 29 ga watan Satumba, 2023.
Daga cikin kamfanonin da suke samar da nasu na’urar sarrafa bayanai dai har wa yau akwai kamfanin Huawei mai nau’in HiSilicon, zubin Kirin 9000. – Jaridar AMINIYA, Jumma’a, 22 ga watan Satumba, 2023.
Daga cikin ƙananan ayyukan wayar salula akwai jirkita bayanan da wayarka ta ɗauko na bidiyo, zuwa asalin hoton bidiyon kai tsaye. Kamar yadda na’urar Image Processing Unit ko IPU ke yi wajen sarrafa bayanan da waya ke ɗaukawa daga kyamara, zuwa asalin hotunan da wayar ta ɗauka. – Jaridar AMINIYA, Jumma’a, 15 ga watan Satumba, 2023.
Ɓangaren SoC ya ƙunshi manyan na’urori guda bakwai ne. Waɗannan na’urori dai su ne ke da alhalin tafiyar da sauran ɓangarorin wayar salula. Shi yasa ma wasu masana ke cewa, cibiyar SoC ce ƙwakwalwar wayar salula. – Jaridar AMINIYA, Jumma’a, 8 ga watan Satumba, 2023.
Kasancewar wayar salula na’ura ce da ake tare da ita a jiki a kowane lokaci, saboda yanayin girmanta (shi yasa ake kiranta da suna “Mobile Phone” – wato wayar da ake tafiya da ita duk inda ake), yasa batirinta na ɗauke ne da sinadaran dake iya riƙe makamashin lantarki an tsawon lokaci, sannan kuma ana iya cajin batirin lokaci zuwa lokaci. – Jaridar AMINIYA, Jumma’a, 1 ga watan Satumba, 2023.
Daga bayanan da suka gabata mai karatu zai fahimci saurin ci gaba da ake samu wajen ingantawa da kuma ƙarfafa girma da mizanin ma’adanar wayar salula, musamman ma’adanar wucin-gadi, wato: “RAM”.
Ma’adanar ROM na iya ɗaukan zallar bayani a sigar rubutu. Tana iya ɗaukan bayanan sauti (Audio). Tana iya ɗaukan hotuna (Images/Pictures). Tana iya ɗaukan hotuna masu motsi, wato bidiyo kenan. – Jaridar AMINIYA, Jumma’a, 18 ga watan Agusta, 2023.
Dukkan wayoyin salula masu amfani da sikirin nau’in LCD suna sarrafa haske da launi ne ta amfani da fasahar “In-Plane Switching”, wato: “IPS”, ko kuma “Plane to Line Switching”, wato: “PLS”. – Jaridar AMINIYA, Jumma’a, 11 ga watan Agusta, 2023.