Baban Sadik

Baban Sadik marubuci ne, kuma mai bincike a fannin Kimiyya da Fasahar Sadarwar zamani da tasirinsu ga al'umma. Ya tanadi wannan shafi ne don taskance dukkan maƙalolin da yake gabatarwa a shafinsa na "Kimiyya da Ƙere-Ƙere" a jaridar AMINIYA wanda ya faro tun shekarar 2006.

Matashiya Kan Mu’amala da Intanet a Wayar Salula

Idan masu karatu basu mance ba, mun yi ta gabatar da bayanai da kasidu kan abin da ya shafi mu’amala da fasahar Intanet a wayar salula a lokuta dabam-daban.  To amma har yanzu akwai sauran rina a kaba.  Domin kusan a duk mako sai na samu sakon text ko wani ya bugo waya ta neman karin bayani kan yadda wannan tsari yake.  Wannan yasa na sake neman lokaci don takaita bayanai masu gamsarwa a karo na karshe in Allah Ya yarda.  Dangane da samun damar mu’amala da fasahar Intanet a wayar salula, akwai matakai ko ka’idoji kamar haka:

Karin Bayani...