![Sakonnin Masu Karatu (2009) (5)](https://babansadik.com/wp-content/uploads/2017/04/tambayoyi.png)
Sakonnin Masu Karatu (2009) (5)
Ga kadan cikin wasikun masu karatu nan kamar yadda muka saba kawowa lokaci-lokaci. Wasu na riga na amsa su tun sadda aka aiko su, wasu kuma nayi alkawarin amsa su ne a wannan shafi; wasu sakonnin kuma ta hanyar wayar tarho aka yi su, na bayar da amsarsu nan take. Don haka wadanda aka bugo don yabo, sai dai muce Allah saka da alheri, don ba zan iya kawo dukkansu ba. Wadannan sakonni dai na text ne ko wadanda aka rubuto ta hanyar Imel, muna kuma kara nuna godiyarmu ga dukkan masu bugowa ko aiko da sako ta dukkan hanyoyin, Allah saka da alheri, ya kuma bar zumunci, amin summa amin. A halin yanzu ga sakonnin nan: