![Tasirin Kimiyyar Sadarwar Zamani a Duniya](https://babansadik.com/wp-content/uploads/2017/03/it-tsarin-siyasa.jpg)
Tasirin Kimiyyar Sadarwar Zamani a Duniya
A yau za mu dubi tasirin fasahar sadarwa na zamani a duniya. A sha karatu lafiya.
Makaloli a fannin kimiyya da fasaha!
A yau za mu dubi tasirin fasahar sadarwa na zamani a duniya. A sha karatu lafiya.
Ga kashi na biyu cikin jerin kasidun da muka fara kawowa makon jiya kan fasahar hasken “Laser” da alakarsa da fannin likitanci.
Daga cikin nau’ukan fasahan dake amfani da haske akwai “Laser Light”, wanda a halin yanzu ake amfani da ita hatta a fannin likitanci. Wannan shi ne abin da za mu duba a wannan mako.
Kasidarmu ta yau dai fadakarwa ce kan samuwar tashoshin tauraron dan adam na gidan rediyon BBC Hasau da DW. A sha karatu lafiya.
Kaddamar da tauraron dan adam da Najeriya tayi mai suna: “NigComSat-1”, yana da fa’idoji da dama da al’umma za su iya samu muddin aka inganta tsarin sosai. A yau za mu dubi daya daga cikin wannan alfanu, kamar yadda hukumar ta tabbatar.
A yau mun dawo don ci gaba da bayani kan tsarin sadarwa ta wayar iska, inda za mu yi bayani kan wani tsari, makamancin tsarin da ya gabata na Bluetooth. Wannan tsari shi ne tsarin sadarwa ta amfani da fasahar sadarwa ta Infra-red. Kamar tsarin sadarwa ta Bluetooth, Infra-red ya kunshi tsarin sadarwa ne daga wani kayan fasahar sadarwa zuwa wani, amma a iya tazarar da bai kai na Bluetooth ba. A yau za mu ji tarihin wannan tsari ; yaushe ya samu, me da me ake yi dashi, yaya tsarin ke kasancewa, wasu irin kayayyakin fasahar sadarwa ne ke amfani dashi, kuma me ye alakar da ke tsakanin fasahar sadarwa ta Bluetooth, da na Infra-red ? Idan mai karatu na tare damu, duk zai samu wadannan bayanai cikin yardar Ubangiji. A biyo mu.
Fasahar GPRS ce ke lura da tsarin aikawa da karban sakonnin hotuna da bidiyo ta siginar rediyon wayar salula. Duk da cewa wannan tsari bai bunkasa a tsakanin kamfanonin sadarwar wayar salula ba, saboda rashin hanyar sadarwa mai inganci, yana da kyau mu san me wannan fasaha take nufi. A sha karatu lafiya.
A makon jiya mun yi tattaki ne zuwa dakin bincike don tsamo bayanai da suka shafi ma’ana, asali, tarihi da kuma bunkasar fasahar sadarwa ta Bluetooth, in da a karshe muka karkare da cewa wannan fahasar sadarwa ta bunkasa ne saboda tasirin ta wajen sawwake aikawa da sakonni daban-daban ta hanya mafi sauki, ba sai an yi ta hakilon jona wayoyi a jikin kayayyakin sadarwa ba. A yau za mu ci gaba da bayani kan nau’ukan kayayyakin da ke dauke da wannan tsarin sadarwa mai kwarjini, da kuma tsarin aikawa da sakonni ta amfani da wannan sabuwar fasaha. Idan hali yayi, za mu zurfafa bayani kan abin daya shafi “ka’idojin sadarwa” (Communication Protocols) da kuma zangunan da ke sawwake wannan tsarin sadarwa, a fasahance, wato Protocol Layers. A biyo mu.
A wannan mako mun dawo da wani sabon fanni, wanda ya kunshi tsarin sadarwa a tsakanin kayayyakin fasahar sadarwa ta amfani da wayar iska, wato abin da a Turance ake kira Wireless Communication. In Allah Ya yarda, za mu yi bayani ne kan tsarin sadarwa ta amfani da fasahar sadarwa ta Bluetooth, na’urar sadarwar da galibi muke dauke da ita a wayar salularmu. Sau tari galibin mu mun dauki cewa wannan fasaha ta sadarwa na dauke ne kawai a wayar salula, don ta hanyar kadai muka san ta. A yau za mu karanta bayanai kan asalin wannan fasaha, yaushe ta bayyana, wa da wa suka kirkiro ta, ina ta samo wannan suna, yaya tsarin sadarwan yake, wasu kayayyakin sadarwa na zamani ne ke dauke da wannan na’ura ko fasaha bayan wayoyin tafi-da-gidanka da muka sani? Duk za mu samu bayanai kan haka a wannan makala. A yanzu ba tare da bata lokaci ba sai a biyo mu.
Ga kashi na uku kuma na karshe, cikin jerin binciken da muke yi kan fasahar “Fibre Optics,” sabuwar fasahar waya dake daukan sinadaran haske don aiwatar da sadarwa.
Ga kashi na biyu cikin jerin binciken da muke yi kan fasahar “Fibre Optics,” sabuwar fasahar waya dake daukan sinadaran haske don aiwatar da sadarwa.
Daga cikin nau’ukan wayoyin dake dauke da sinadaran sadarwa a zamanin yau akwai nau’in “Fibre Optics”, wanda ke samuwa ta hanyar gilasai da ake nikewa a dama shi kamar kunu. Daga wannan mako za mu fara bincike don fayyace hakikanin wannan sabuwar fasaha. Wannan shi ne kashi na farko. A sha karatu lafiya.