![Tsokaci Kan Sabuwar Dokar Ta’ammali Da Kafafen Sadarwa na Zamani a Najeriya (1)](https://babansadik.com/wp-content/uploads/2022/07/dokar-NITDA-1.jpeg)
Tsokaci Kan Sabuwar Dokar Ta’ammali Da Kafafen Sadarwa na Zamani a Najeriya (1)
Manyan al’amuran da wannan doka ta shagaltu dasu dai guda biyu ne: na farko shi ne ayyukan dukkan kafafen sadarwa na zamani dake Intanet, wadanda ‘yan Najeriya ke amfani dasu; suna da rajista ne, ko babu rajista. Wadannan kafafe kuwa, kamar yadda na ayyana a baya, su ne kafafen sada zumunta, irin su Facebook, da Twitter, da Google (Youtube), da WhatsApp (Facebook/Meta), da kuma dukkan jami’ai ko wakilansu a Najeriya. Sai abu na biyu, wato tabbatar da hanyoyin kariya ga ‘yan Najeriya da ma baki, a kafafen sadarwa na zamani. – Jaridar AMINIYA, Jumma’a, 1 ga watan Yuli, 2022.