Nau’ukan Cutar Kwamfuta

Idan mai karatu na tare da mu, muna yin bayani ne kan kwayoyin cutar kwamfuta da illolin su da kuma masu hakki wajen kirkiro wannan annoba.  Har wa yau, a makon da ya gabata mun kawo bayanai kan tsarin da masu wannan al’ada ke bi wajen yada kwayoyin cutar da ke ma kwamfuta illa a duniya.  A karshe kuma mai karatu ya samu bayanai kan tasirin wannan sana’a nasu, hatta ga siyasar duniya.  A yau za mu ci gaba, inda za mu kawo hanyoyin da wadannan masana harkan kwamfuta ke bi wajen shiga kwamfutocin jama’a; ko dai don yada kwayoyin cuta, ko aiwatar da satan bayanai, ko kuma don sace ma jama’a kudade da kuma aikin leken asiri. 

Karin Bayani...

Ma’ana da Asalin Kwayar Cutar Kwamfuta (Virus)

Daga wannan mako in Allah Ya yarda, za mu fara bayanai kan manyan matsalolin da ke damun kwamfuta da masu amfani da ita a wannan zamani da muke musamman.  Kamar dai yadda dan Adam yake ne; yana da damuwoyi da dama da ke masa kaidi wajen tafiyar da rayuwa ingantacciya kuma cikin sauki.  Haka na’urar kwamfuta take; akwai matsaloli da ke mata karan-tsaye wajen gudanar da ayyukan da aka kera ta don yin su, cikin sauki.  Wadannan matsaloli suna da yawa, amma za mu dauki wadanda suka shafi lafiyarta da kwakwalwarta ne kadai, don su ne manyan matsalolin da suka fi kowanne tasiri wajen dama mata lissafi, musamman cikin wannan zamani da aka samu kwararru kan ilimin ta, birjik a duniya.

Karin Bayani...

Mu Leka Duniyar ‘Yan Dandatsa (Hackers) (1)

‘Yan Dandatsa kwararru ne kan harkar kwamfuta da abin da ya shafi ruhinta, masu amfani da kwarewarsu wajen shiga kwamfutocin mutane ba tare da izni ba, a nesa ne ko a kusa ; masu aiko ma kwamfutoci cututtuka da dama, don satan bayanai ko aikin leken asiri.  A takaice dai mutane ne masu mummunar manufa wajen kwarewarsu.  A yau za mu leka duniyarsu ne don sanin hakikanin tsarin rayuwarsu : irin sunaye ko lakubbansu, gidajen yanar sadarwarsu, shahararrun littafai kan aikinsu, dabi’unsu da addininsu na dandatsanci da kuma shahararru cikin finafinan da aka yi kan sana’arsu. Ga fili ga mai doki.

Karin Bayani...