Sakonnin Masu Karatu (2009) (8)

A yau ma ga mu dauke da wasu cikin wasikun masu karatu. Kamar yadda muka sha fada kwanakin baya, cewa za mu daina amsa maimaitattun tambayoyi, don kauce wa tsawaitawa.  Duk wanda ke son yin tambaya, in da hali, zai dace ya binciki kasidun baya da ke mudawwanar wannan shafi a http://fasahar-intanet.blogspot.com, don samun gamsuwa.  A halin yanzu ga wadanda kuka aiko mana nan makonnin baya:

Karin Bayani...

Sakonnin Masu Karatu (2009) (1)

A kasidar da ta gabata wancan mako, mun kawo bayanai kan yadda kwamfuta take, da karikitanta da kuma ruhin, ko ran da ke gudanar da rayuwarta gaba data.  Har daga karshe muka sanar da mai karatu cewa asalin masu kera gangar-jikin kwamfuta, wato Hardware, sune kwararru kan kimiyyar lantarki (Electrical Engineers).  A yayin da Computer Programmers, a nasu  bangaren, ke da hakkin ginawa da kuma dora mata ruhin da ke taimaka mata gudanar da ayyukanta gaba daya, wato Software.  Bamu karkare kasidar ba sai da muka kawo rabe-rabe da kuma dukkan nau’ukan kowannensu.  A yau kuma ga mu dauke da amsoshi kan wasu daga cikin tambayoyin da masu karatu suka aiko.

Karin Bayani...

Matashiya Kan Mu’amala da Intanet a Wayar Salula

Idan masu karatu basu mance ba, mun yi ta gabatar da bayanai da kasidu kan abin da ya shafi mu’amala da fasahar Intanet a wayar salula a lokuta dabam-daban.  To amma har yanzu akwai sauran rina a kaba.  Domin kusan a duk mako sai na samu sakon text ko wani ya bugo waya ta neman karin bayani kan yadda wannan tsari yake.  Wannan yasa na sake neman lokaci don takaita bayanai masu gamsarwa a karo na karshe in Allah Ya yarda.  Dangane da samun damar mu’amala da fasahar Intanet a wayar salula, akwai matakai ko ka’idoji kamar haka:

Karin Bayani...