A wannan mako mun dawo da wani sabon fanni, wanda ya kunshi tsarin sadarwa a tsakanin kayayyakin fasahar sadarwa ta amfani da wayar iska, wato abin da a Turance ake kira Wireless Communication. In Allah Ya yarda, za mu yi bayani ne kan tsarin sadarwa ta amfani da fasahar sadarwa ta Bluetooth, na’urar sadarwar da galibi muke dauke da ita a wayar salularmu. Sau tari galibin mu mun dauki cewa wannan fasaha ta sadarwa na dauke ne kawai a wayar salula, don ta hanyar kadai muka san ta. A yau za mu karanta bayanai kan asalin wannan fasaha, yaushe ta bayyana, wa da wa suka kirkiro ta, ina ta samo wannan suna, yaya tsarin sadarwan yake, wasu kayayyakin sadarwa na zamani ne ke dauke da wannan na’ura ko fasaha bayan wayoyin tafi-da-gidanka da muka sani? Duk za mu samu bayanai kan haka a wannan makala. A yanzu ba tare da bata lokaci ba sai a biyo mu.