Baban Sadik

Baban Sadik marubuci ne, kuma mai bincike a fannin Kimiyya da Fasahar Sadarwar zamani da tasirinsu ga al'umma. Ya tanadi wannan shafi ne don taskance dukkan maƙalolin da yake gabatarwa a shafinsa na "Kimiyya da Ƙere-Ƙere" a jaridar AMINIYA wanda ya faro tun shekarar 2006.

Kimiyyar Kur’ani Da Ta Zamani: A Ina Aka Hadu? (1)

Mun samu tambaya daga daya daga cikin masu karatu, wanda yake son sanin alakar dake tsakanin fahimtar malaman kimiyya na zamani kan abubuwan da suka shafi kimiyya, da kuma bayanin wasu abubuwa na kimiyya da Al-Kur’ani mai girma yayi. Shin, a ina suka hadu kuma a ina suka rabu? Wannan shi ne abin da zamu fara rubutu a kai daga wannan mako illa maa sha Allahu. A sha karatu lafiya.

Karin Bayani...

Tasirin Fasahar Intanet Ga Kwakwalwar Dan Adam (2)

A makon da ya gabata ne idan masu karatu ba su mance ba, mu ka fara jero bayanai kan irin tasirin da Fasahar Intanet ke yi ga kwakwalwar dan Adam, saboda irin mu’amalar da ya ke yi da wannan fasaha.  Mun yi bayanin irin dalilan da ke haddasa tasirin, da kuma cewa lallai akwai alaka tabbatacciya mai kama da kawalwalniya, wacce ke samuwa tsakanin kwakwalwar dan Adam da kuma asalin duniyar da yake ciki.  Mun nuna cewa wannan alaka na samuwa ne sanadiyyar tasirin wannan fasaha da kwakwalwar mai mu’amala.  Daga karshe mu ka yi alkawarin kawo abin da hakan ke haifarwa, da yadda za a iya magance wata matsala idan akwai.  Saboda yanayin tsarin da bayanan su ka zo, mun ce mai karatu ba zai fahimci in da aka dosa gaba daya ba, sai a wannan mako.  Mu na kuma fatan hakan.  Don haka yanzu  za mu ci gaba.

Karin Bayani...