![Sakonnin Masu Karatu (2019) (4)](https://babansadik.com/wp-content/uploads/2018/10/Tambayoyi2.png)
Sakonnin Masu Karatu (2019) (4)
Ci gaban sakonnin masu karatu da na samu a wannan shekara. An buga wannan bayani ne a jaridar AMINIYA na watan Fabrairu, 2019.
Makaloli a fannin kimiyya da fasaha!
Ci gaban sakonnin masu karatu da na samu a wannan shekara. An buga wannan bayani ne a jaridar AMINIYA na watan Fabrairu, 2019.
Ci gaban sakonnin masu karatu. A sha karatu lafiya.
A yau kuma, kamar yadda muka saba lokaci zuwa lokaci, ga mu dauke da sakonninku da kuka aiko to tes. Galibin sakonnin da nake samu ta Imel nan take nake amsa su, musamman idan ba suna dauke ne da wasu bukatu da ke bukatar doguwar bincike ba. Bayan haka, idan sako ya sha maimaituwa ba na amsa shi. Don haka sai dai a yi hakuri. Idan muka ce za mu rika maimata tambayoyi, musamman ma wadanda suka sha maimaituwa a wannan shafi, a gaskiya ba za mu ci gaba ba. Da fatan za a yi hakuri da wannan ka’ida. A yanzu dai ga abin da ya sawwaka.
Wannan kashi na takwas kenan cikin fadakarwar da muka faro a makon jiya kan hanyoyin da mai karatu zai iya kwarewa a fannin kimiyya da fasahar sadarwa na zamani. A yau mun dubi fannin “System Networking” ne.
A cikin kasidar da ta gabata makon jiya ne mai karatu ya samu bayanai kan tsarin sadarwa a tsakanin kwamfutoci, abin daa Turance ake kira Computer Networking. Bayan ‘yar gajeriyar gabatarwa, mun kawo bayani kan ma’ana da kuma nau’ukan tsarin sadarwan da ke tsakanin kwamfutoci, inda daga karshe muka nuna ma mai karatu cewa samun cikakkiyar fahimta kan irin tsarin da kwamfutoci ke sadar da bayanai a tsakaninsu ba abu bane mai sauki, musamman ma ganin cewa kashi sittin ko sama da haka na alakar da ke tsakanin ruhin kowace irin na’ura ta sadarwa da gangar-jikinta, ba alaka bace da za a iya gani a zahiri, sam. Don haka sai dai kawai a kwatanta ma mai karatu don ya samu kiyastaccen tsarin a kwakwalwarsa. Amma duk da haka, wannan alaka na nan, kuma tabbatacciya ce.
Fasahar Intanet ta samo asali ne sanadiyyar musayar bayanai da kwamfutoci ke yi a tsakaninsu. Yau za mu dubi yadda kwamfutoci ke aiwatar da irin wannan sadarwa, wanda ya sauya duniya ta bangaren sadarwa.