Tag: Imel
![Sakonnin Masu Karatu (2009) (8)](https://babansadik.com/wp-content/uploads/2017/04/tambayoyi.png)
Sakonnin Masu Karatu (2009) (8)
A yau ma ga mu dauke da wasu cikin wasikun masu karatu. Kamar yadda muka sha fada kwanakin baya, cewa za mu daina amsa maimaitattun tambayoyi, don kauce wa tsawaitawa. Duk wanda ke son yin tambaya, in da hali, zai dace ya binciki kasidun baya da ke mudawwanar wannan shafi a http://fasahar-intanet.blogspot.com, don samun gamsuwa. A halin yanzu ga wadanda kuka aiko mana nan makonnin baya:
![Shahararren Dan Dandatsa, “Alan Ralsky” Ya Shiga Hannu](https://babansadik.com/wp-content/uploads/2017/03/Alan-Ralsky.jpg)
Shahararren Dan Dandatsa, “Alan Ralsky” Ya Shiga Hannu
Labaru da dumi-duminsu na tabbatar da cewa shahararren dan dandatsan nan mai suna Alan Ralsky, ya shiga hannun hukuma. A yau za mu dubi irin laifuffukan da yayi ne a baya, da yadda aka yi hukuma ta samu nasara a kansa, da kuma abin da ke jiransa na hukunci. A sha karatu lafiya.
![“Spam”: Sakonnin Bogi na Imel](https://babansadik.com/wp-content/uploads/2017/03/spam.jpg)
“Spam”: Sakonnin Bogi na Imel
Sakonnin bogi na cikin abubuwan da suka fi yawaita a a bangaren sakonnin Imel da mutane ke karba. Kuma galibi ire-iren wadannan sakonnin na zuwa ne daga kafofi da dama….da kasuwanci, da masu zamba cikin aminci. A wannan mako za mu dubi wannan matsala a mahangar bincike na asali da wadanda ke aiko su, da hanyoyin da suke bi wajen samun adireshin mutane.
![Ka’idojin Sadarwa ta Imel (2)](https://babansadik.com/wp-content/uploads/2017/03/imel.jpg)
Ka’idojin Sadarwa ta Imel (2)
Wannan shi ne kashi na biyu cikin kasidun da muka faro bayanai kan ka’idojin sadarwa dake tafiyar da fasahar Imel. A makon jiya mun yi gabatarwa a kashi na daya. A sha karatu lafiya.
![Ka’idojin Sadarwa ta Imel (1)](https://babansadik.com/wp-content/uploads/2017/03/imel-2.jpg)
Ka’idojin Sadarwa ta Imel (1)
Tsarin sadarwa na Imel na tattare da wasu ka’idoji ne dake tabbatar dashi. A wannan kasida da wacce ke biye da ita a makon gaba, za mu dubi wadannan ka’idoji ne a kimiyyance, kuma a fasahance. Wannan ke nuna lallai akwai tsari cikin al’amarin sadarwa na zamani.
- 1
- 2