![Yawaitar Motoci Masu Makamashin Lantarki a Duniya: Ina Muka Dosa? (2)](https://babansadik.com/wp-content/uploads/2017/10/lantarki-5.jpg)
Yawaitar Motoci Masu Makamashin Lantarki a Duniya: Ina Muka Dosa? (2)
Kasar Sin ta ba da sanarwar daina amfani da motoci masu amfani da makamashin man fetur da dizil a kasarta zuwa shekarar 2040. A makon jiya mun fara yin nazari kan sakon dake dunkule cikin wannan sanarwa nata, da kasashen da suka yi wanann kuduri kanfinta, da sakamakon hakan ga kudaden shigarmu a Najeriya, sannan a karshe muji bayani kan motoci masu amfani da makamashin lantarki da yanayinsu. Ga kashi na biyu cikin wannan nazari namu nan. A sha karatu lafiya.