Cikin bayanan da muka fara kwararowa kan Kwayar Cutar Kwamfuta da nau’ukan ta da kuma yadda take haddasuwa, da masu kirkiran ta, mun tsaya ne a gabar da ke karantar da mu irin manufofin da masu wannan sana’a ke tinkaho dasu wajen yin dukkan wata ta’addanci da ta shafi cutar da kwamfutocin mutane a duniya. A yau za mu ci gaba, in da mai karatu zai ji bayani kan ire-iren ayyukan da wadannan ‘Yan Dandatsa (Hackers) suke yi wajen yada wadannan cututtuka da suke kirkira. Bayan haka, za kuma muji irin tasirin da hakan ke yi a duniyar yau. Kada mai karatu ya mance cewa a cikin kasidun da suka gabata, mun nuna cewa wannan sana’a ta Dandatsanci (Hacking), ta yadu sosai musamman cikin manyan kasashen da suka ci gaba wajen tsarin sadarwa ta zamani, irin su Amurka, Ingila, Awstiraliya, Sin, Jamus, Rasha da Jafan. Ina mana wannan matashiya ne don mu dada fahimtar yadda tasirin ayyukan su na Dandatsanci ke cin karensa ba babbaka a yau, kamar yadda za mu karanta a yau. Mu je zuwa, wai mahaukaci ya hau Kura.