![Web 3.0: Sabon Nau’in Giza-Gizan Sadarwa na Duniya Zubi na Uku (1)](https://babansadik.com/wp-content/uploads/2022/03/web-3.0-1.jpg)
Web 3.0: Sabon Nau’in Giza-Gizan Sadarwa na Duniya Zubi na Uku (1)
Wannan nau’i na zubin giza-gizan sadarwa ya samo asali ne tsakanin shekarun karshe na 1980s zuwa karshen shekara ta 2000. Wannan shi ne zamanin jarirantakar fasahar Intanet, kuma marhalar dake tsakanin sadda hukumar tsaro ta Amurka ta yafuce tsarin ARPANET daga giza-gizan sadarwar kasar, don bambanceshi da na gama-gari. – Jaridar AMNIYA, Jumma’a, 4 ga watan Maris, 2022.