Sakonnin Masu Karatu (2009) (12)
Ci gaban sakonnin masu karatu. A sha karatu lafiya.
Makaloli a fannin kimiyya da fasaha!
Ci gaban sakonnin masu karatu. A sha karatu lafiya.
A yau za mu karasa bayani kan sauran shahararrun manhajojin da suka ci duniya (kuma suke kan ci a yanzu) a duniyar Intanet, wajen aiwatar da wadannan aikace-aikace na cutarwa. Sai dai kuma, sabanin yadda nace a makon da ya gabata, ba za mu iya karkare bayanai cikin wannan mako ba, sai zuwa makonni uku nan gaba in Allah Ya yarda.
Idan mai karatu na tare da mu, muna yin bayani ne kan kwayoyin cutar kwamfuta da illolin su da kuma masu hakki wajen kirkiro wannan annoba. Har wa yau, a makon da ya gabata mun kawo bayanai kan tsarin da masu wannan al’ada ke bi wajen yada kwayoyin cutar da ke ma kwamfuta illa a duniya. A karshe kuma mai karatu ya samu bayanai kan tasirin wannan sana’a nasu, hatta ga siyasar duniya. A yau za mu ci gaba, inda za mu kawo hanyoyin da wadannan masana harkan kwamfuta ke bi wajen shiga kwamfutocin jama’a; ko dai don yada kwayoyin cuta, ko aiwatar da satan bayanai, ko kuma don sace ma jama’a kudade da kuma aikin leken asiri.