![Shawarwari Ga Gwamnatin Tarayya Kan Hanyoyin Ciyar Da Najeriya Gaba A Fannin Kimiyya Da Ƙere-Ƙere (4)](https://babansadik.com/wp-content/uploads/2023/10/science-4.jpg)
Shawarwari Ga Gwamnatin Tarayya Kan Hanyoyin Ciyar Da Najeriya Gaba A Fannin Kimiyya Da Ƙere-Ƙere (4)
Hukumar Burtaniya ta taimaka wajen shigowa da bindigogi, da kayayyakin alatun ɗaki, da kekunan hawa, da takalma, kai hatta ababen shaye-shaye na barasa ta taimaka wajen shigowa da su. A wasu bangarorin Najeriya – musamman kudanci – hukumar mulkin mallaka ta haramta sayarwa da shan giyar “gwaggwaro” wacce ake tsimawa a kauyuka. – Jaridar AMINIYA, Jumma’a, 7 ga watan Yuli, 2023.