
Hira da Tattaunawa a Intanet
A ƙasidar da ta gabata wancan mako, mun karanta cewa Wasikar Hanyar Sadarwa wato Imel, na ɗaya daga cikin gimshikan da suka dada habbaka sanayya kan Fasahar Intanet a duniya gaba. To bayan Imel, masu biye mata sune Zaurorin Hira da Majalisun Tattaunawa. Dunƙulallen sunan da suka fi shahara dashi shi ne Cyber Communities, ko kace Ƙauyukan Yanar Gizo, a Hausance.