![Tasirin Ci Gaban Kimiyya da Fasaha Ga Rayuwa da Zamantakewar Dan Adam a Duniya (4)](https://babansadik.com/wp-content/uploads/2021/05/ci-gaba-4.jpeg)
Tasirin Ci Gaban Kimiyya da Fasaha Ga Rayuwa da Zamantakewar Dan Adam a Duniya (4)
An buga wannan makala ne a Jaridar AMINIYA ta ranar Jumma’a, 24 ga watan Janairu, 2020.
Makaloli a fannin kimiyya da fasaha!
An buga wannan makala ne a Jaridar AMINIYA ta ranar Jumma’a, 24 ga watan Janairu, 2020.
Asali da Bunkasa Duk da cewa bincike na hakika a tsarin binciken kimiyya na zamani kan wannan fannin ilmi bai shige shekaru ashirin da wani abu ba, sai dai idan muka yi la’akari da tsarin zamantakewar dan adam a wannan duniya, dangane da tarihi, za mu samu shi ma tsohon fannin ilmi ne kamar sauran…
A kashi na biyu nayi yunkurin fassara wasu kalmomi ne masu alaka da wannan fanni. Wadannan kalmomi za su ci gaba da bayyana a cikin kasidun da za su no nan gaba. Sai a kiyaye.
A yau za mu fara nazari na musamman mai zurfi kan sinadaran dabi’ar halitta. Wannan fanni ne dake lura da siffofi na dabi’un halitta da a turance ake kira: “Genetics.” Yanayin rubutun, da harshen da nayi amfani dashi, yana da sarkakiya kadan, saboda tsaurin dake cikin ilimin ne. Don haka a natsu wajen karatu, za a fahimta in Allah Yaso.