![Fasahar Sadarwa ta Bluetooth (2)](https://babansadik.com/wp-content/uploads/2017/03/bluetooth-2.jpg)
Fasahar Sadarwa ta Bluetooth (2)
A makon jiya mun yi tattaki ne zuwa dakin bincike don tsamo bayanai da suka shafi ma’ana, asali, tarihi da kuma bunkasar fasahar sadarwa ta Bluetooth, in da a karshe muka karkare da cewa wannan fahasar sadarwa ta bunkasa ne saboda tasirin ta wajen sawwake aikawa da sakonni daban-daban ta hanya mafi sauki, ba sai an yi ta hakilon jona wayoyi a jikin kayayyakin sadarwa ba. A yau za mu ci gaba da bayani kan nau’ukan kayayyakin da ke dauke da wannan tsarin sadarwa mai kwarjini, da kuma tsarin aikawa da sakonni ta amfani da wannan sabuwar fasaha. Idan hali yayi, za mu zurfafa bayani kan abin daya shafi “ka’idojin sadarwa” (Communication Protocols) da kuma zangunan da ke sawwake wannan tsarin sadarwa, a fasahance, wato Protocol Layers. A biyo mu.