Sakonnin Masu Karatu (2010) (2)

A yau kuma ga mu dauke da sakonnin da kuka aiko daga ranar bikin sallar azumi da ya gabata, zuwa ranar litinin din wannan mako.  Duk sakonnin gaisuwar salla ba su bukatar wani jawabi, don haka na jero su a farko.  Kamar sauran lokuta, akwai wadanda suka bugo waya, da yawa ba kadan ba.  Muna musu godiya kan haka.  Wadanda suka aiko sakonnin Imel kuma za su gafarce ni, sai mako mai zuwa zan buga sakonninsu in Allah Ya so.  A halin yanzu ga dan abin da ya samu.  A sha karatu lafiya.

Karin Bayani...

Tsarin Fasahar Faifan CD (1)

A cikin kashi na farko da muka gabatar mai taken: “Tarihin Ma’adanar Bayanan Sadarwa” watanni biyu da suka gabata, mai karatu ya samu mukaddima kan yadda dan Adam ya fara wayar da kansa sanadiyyar kalu-balen rayuwa da yake samu yau da gobe, cikin abinda ya shafi tsarin adanawa da kuma taskance bayanai; daga taskance su a kwakwalwansa, zuwa taskance su cikin ababen da ke muhallinsa.

A karshe dai, sabanin lokutan baya, a wannan zamani dan Adam ya nemo wasu hanyoyi masu sauki da ban mamaki da yake bi wajen taskance bayanai, da kuma nemo su cikin sauki ba tare da matsala ba. Dangane da haka muka ce zamu yi nazari na musamman kan ire-iren wadannan hanyoyi ko kayayyakin adanawa da kuma taskance bayanai da dan Adam ya kirkira, inda za mu fara da dubi kan tsari da kuma kimtsin da ke cikin Fasahar Faifan CD, watau Compact Disc Technology kenan a Turance. Amma kafin mu dulmiya kan tsarin Fasahar Faifan CD, zai dace mu yi waiwaye, abinda Malam Bahaushe ke kira “adon tafiya”.

Karin Bayani...