![Nazari Kan Karin Harajin Kudin Kiran Waya Da Na “Data”](https://babansadik.com/wp-content/uploads/2022/08/NCC-Umar-Danbatta.jpg)
Nazari Kan Karin Harajin Kudin Kiran Waya Da Na “Data”
An kiyasta cewa idan wannan sabuwar doka ta Karin haraji ta fara aiki, kamfanonin wayar salula za su kara yawan kudin da suke caja na kiran waya a duk minti guda; daga naira ashirin (N20.00) ko kasa da haka da suke cira a yanzu, zuwa naira arba’in (N40.00). Haka ma, gigabyte 1 na “data” da a yanzu ake saya a kan naira dubu daya (N1,000.00) a misali, zai koma naira dubu biyu da dari biyar (N2,500.00). – Jaridar AMINIYA, Jumma’a, 19 ga watan Agusta, 2022.