![Sakonnin Masu Karatu (2011) (8)](https://babansadik.com/wp-content/uploads/2017/04/tambayoyi.png)
Sakonnin Masu Karatu (2011) (8)
A yau kuma ga mu dauke da wasu daga cikin tambayoyinku da kuka aiko ta wayar salula da hanyar Imel. Kamar yadda na sha sanarwa dai, duk tambayar da na riga na amsa ta a lokacin da aka aiko ban cika kawo su ba. Sai in na ga akwai wata fa’ida mai gamewa ga sauran masu karatu. Domin wasu kan rubuto tambaya su ce in bamu amsar ta wayar salularsu ko adireshin Imel dinsu, kada in jira sai lokacin amsa tambayoyi a shafin jaridar. Wasu kuma tambayoyinsu na bukatar amsa ne nan take, saboda irin matsalar da ke dauke cikin tambayar, wacce ke bukatar a warwareta nan take. Allah mana jagora, amin.