![Tsarin Neman Bayanai a Intanet (1)](https://babansadik.com/wp-content/uploads/2017/03/bincike-intanet-1.jpg)
Tsarin Neman Bayanai a Intanet (1)
A baya in masu karatu basu mance ba, munyi bayani kan manhajar dake taimakawa wajen zakulo bayanai daga shafukan Intanet. A yau za mu dubi dabaru da hanyoyin da ake amfani dasu wajen yin hakan, cikin sauki.
Makaloli a fannin kimiyya da fasaha!
A baya in masu karatu basu mance ba, munyi bayani kan manhajar dake taimakawa wajen zakulo bayanai daga shafukan Intanet. A yau za mu dubi dabaru da hanyoyin da ake amfani dasu wajen yin hakan, cikin sauki.
Duk da cewa babu wata kasa ta musamman da za ta tinkaho da mallakar fasahar Intanet a duniya, akwai wasu kungiyoyi masu zaman kansu dake lura da tsarin da wannan fasaha take gudanuwa a kai. A wannan mako zamu yi bayani ne ka wadannan kungiyoyi da irin hanyar da suke bi wajen aiwatar da ayyukansu.
Wannan kashi na biyu ne na kasidar da ta gabata a makon jiya. Mun kawo samfurin manhajar Intanet Explorer na kamfanin Microsoft ne. A sha karatu lafiya
A wannan mako na duba mana manhajar da ake amfani da ita ne wajen hawa shafukan Intanet, wato: “Rariyar Lilo” kenan. Ko kace: “Web Browser.”
A makon da ya gabata idan masu karatu basu mance ba, mun kawo bayanai kan tsarin da masu tashoshin talabijin suke bi ne wajen yada shirye-shiryensu, da kuma nau’ukan shirye-shiryen da suke da su a shafukan Intanet. Wannan mako, kamar yadda muka yi alkawari, zamu dubi hanyar sadarwa ta jarida ce da mujallu da suka mamaye giza-gizan sadarwa ta Intanet, kamar wutar daji. Har wa yau, za mu dubi irin tsarin da suke bi wajen yada labarai da kasidu da makaloli. Idan shafuka basu mana halinsu ba, zamu kawo wasu daga cikin jaridun da ke da shafukan yanar gizo a Intanet.
A makon da ya gabata mun fara kawo bayanai kan tsarin da ke tattare da yada labarai da wakoki a gidajen yanar sadarwa na tashoshin rediyo da ake dasu a giza-gizan sadarwa ta duniya. Mun kuma nuna irin hanyoyin da su ke bi wajen taskance labaran musamman ga tashoshin FM masu sayar da wakoki ko kuma yada taskantattun shirye-shiryen su. Har wa yau, ba mu karkare wancan mako ba sai da muka tabbatar da cewa mun kawo bayanai kan dukkan makale-makalen da suka dace mai son sauraron labarai da shirye-shiryen tashoshin rediyo ta Intanet ke bukata kafin yayi hakan. A yau kuma cikin yardan Ubangiji za mu kama hanya in da za mu ji irin tsarin da masu tashoshin Talabijin ke bi a nasu harkan.
Mun fara kawo mukaddima a makon da ya gabata kan nau’ukan fasahar sadarwa da ke giza-gizan sadarwa na Intanet. Inda muka fara da irin dalilan da suka haddasa yaduwar nau’ukan wadannan hanyoyin sadarwa a Intanet, duk da cewa suna da nasu muhallin da su ke ta taka rawa shekaru kusan hamsin da suka gabata. A yau muka ce za mu ci gaba da koro bayanai kan ire-iren wadannan nau’ukan hanyoyin sadarwa, da tsarin da suke gudanuwa a kai da kuma yadda mai karatu zai iya amfana da wadannan hanyoyi ba tare da ya mallaki nau’urorin da ake sauraro ko saduwa da su ba. Bisimillah, wai an hada Malamai kokawa:
Akwai nau’ukan hanyoyin sadarwa dake cikin Intanet, kamar su talabijin da rediyo da jaridu. Daga wannan mako za mu dubi wadannan hanyoyin sadarwa, da tsarinsu a Intanet da kuma irin fasahar da suke dauke dashi.
Idan mai karatu bai mance ba, a makon da ya gabata mun kawo bayanai ne kan Mudawwanar Intanet, wato Web Log, a turance, da tarihinta da kuma yadda ake mallakar mudawwana ga duk mai son yada nasa ra’yin don wasu su karanta a giza-gizan sadarwa ta duniya. Na san da dama cikin masu karatu sun fara himma wajen gina nasu mudawwanar, sakamakon sakonnin da nai ta samu ta Imel da wayar salula da kuma bugowa ma da wasu suka yi, don neman Karin bayani. Haka ake so daman. Wannan na daga cikin abin da nai ta jaddada mana cikin kasidar Waiwaye Adon Tafiya, wato kwatanta abin da aka koya ko karanta, a aikace. Da haka harkan ilimi ya ci gaba a duniya gaba daya. Don haka duk wanda ya fara ginawa, to ya natsu ya karasa. Wanda bai fara ba, ya fara. Wanda kuma ya gama ginawa, ya aiko mana da adireshin don mu ziyarce shi, mu ga abin da yake tallata ma duniya a tsarin tunaninsa. A yau za muci gaba da bayanai kan Mudawwana har wa yau, sai dai za mudan maimaita wasu gabobin bayanan da muka yi, kafin mu zarce, don na fahimci wasu na samun matsala.
Daga cikin hanyoyin fadin albarkacin baki a Intanet akwai Mudawwana, ko Blog a turance. A yau mun dubi wannan manhaja da tsari ne.
Manhajar “Matambayi Ba Ya Bata” ita ce ke taimakawa wajen zakulo bayanai a ko ina suke adane a gidajen yanar sadarwa na duniya. A yau zamu dubi wannan manhaja ne, da amfaninta, da kuma misalai na wasu kamfanoni guda uku.
A wannan mako dai mun dubi rahoton Hukumar Sadarwar Tarho ta Duniya ne, wato: “International Telecommunication Union” (ITU), kan adadin masu mu’amala da Intanet a duniya. A sha karatu lafiya.