![Tsarin Fasahar Faifan CD (2)](https://babansadik.com/wp-content/uploads/2017/04/maadana-3.jpg)
Tsarin Fasahar Faifan CD (2)
Wannan ita ce kasida ta uku cikin jerin kasidun dake bayani kan ma’adanar bayanai, kuma ta biyu kan abin da ya shafi ma’adanar faifan CD, wato: “CD Plates”. A sha karatu lafiya.
Makaloli a fannin kimiyya da fasaha!
Wannan ita ce kasida ta uku cikin jerin kasidun dake bayani kan ma’adanar bayanai, kuma ta biyu kan abin da ya shafi ma’adanar faifan CD, wato: “CD Plates”. A sha karatu lafiya.
A cikin kashi na farko da muka gabatar mai taken: “Tarihin Ma’adanar Bayanan Sadarwa” watanni biyu da suka gabata, mai karatu ya samu mukaddima kan yadda dan Adam ya fara wayar da kansa sanadiyyar kalu-balen rayuwa da yake samu yau da gobe, cikin abinda ya shafi tsarin adanawa da kuma taskance bayanai; daga taskance su a kwakwalwansa, zuwa taskance su cikin ababen da ke muhallinsa.
A karshe dai, sabanin lokutan baya, a wannan zamani dan Adam ya nemo wasu hanyoyi masu sauki da ban mamaki da yake bi wajen taskance bayanai, da kuma nemo su cikin sauki ba tare da matsala ba. Dangane da haka muka ce zamu yi nazari na musamman kan ire-iren wadannan hanyoyi ko kayayyakin adanawa da kuma taskance bayanai da dan Adam ya kirkira, inda za mu fara da dubi kan tsari da kuma kimtsin da ke cikin Fasahar Faifan CD, watau Compact Disc Technology kenan a Turance. Amma kafin mu dulmiya kan tsarin Fasahar Faifan CD, zai dace mu yi waiwaye, abinda Malam Bahaushe ke kira “adon tafiya”.
Bincike na musamman kan ma’adanar bayanai. Ina sa ran ci gaba da wannan nazari nan gaba. Wannan kashi na daya ne.
Sanadiyyar matsalolin da wannan nau’i na babbar manhaja take dashi, jama’a da dama sun fara kaurace mata. Bayanai na nuna cewa hakika kamfanin Microsoft yayi kuskure wajen fitar da ita. Nan gaba ana tunanin zai fitar da wata babbar manhajar, don ceto kwastomominsa.
Ga hanyoyin magance zazzabin kwamfuta idan ta samu matsala.
Kashi na biyu na kasidar dake duba kamaiceceniya tsakanin Windows XP da Windows Vista.
A yau za mu dubi siffofin manyan babbar manhajar kwamfuta biyu na kamfanin Microsoft, da Windows XP da Windows Vista. Wannan zai taimaka wa mai karatu kara sanayya kan wadannan manhajoji masu mahimmanci.
Douglas Engelbart shi ne wanda ya kirkiri na’urar beran kwamfuta, kuma Allah ya masa rasuwa cikin ‘yan kwanakin nan. A yau za mu duba tarihinsa ne da yadda aka yi ya kirkiri wannan na’ura mai tasiri.
A cikin kasidar da ta gabata makon jiya ne mai karatu ya samu bayanai kan tsarin sadarwa a tsakanin kwamfutoci, abin daa Turance ake kira Computer Networking. Bayan ‘yar gajeriyar gabatarwa, mun kawo bayani kan ma’ana da kuma nau’ukan tsarin sadarwan da ke tsakanin kwamfutoci, inda daga karshe muka nuna ma mai karatu cewa samun cikakkiyar fahimta kan irin tsarin da kwamfutoci ke sadar da bayanai a tsakaninsu ba abu bane mai sauki, musamman ma ganin cewa kashi sittin ko sama da haka na alakar da ke tsakanin ruhin kowace irin na’ura ta sadarwa da gangar-jikinta, ba alaka bace da za a iya gani a zahiri, sam. Don haka sai dai kawai a kwatanta ma mai karatu don ya samu kiyastaccen tsarin a kwakwalwarsa. Amma duk da haka, wannan alaka na nan, kuma tabbatacciya ce.
Fasahar Intanet ta samo asali ne sanadiyyar musayar bayanai da kwamfutoci ke yi a tsakaninsu. Yau za mu dubi yadda kwamfutoci ke aiwatar da irin wannan sadarwa, wanda ya sauya duniya ta bangaren sadarwa.
Kashi na biyu cikin nazarin da muka faro kan kwamfuta da dukkan bangarorinta mahimmai. A sha karatu lafiya.
A yau kuma ga mu dauke da bayanai, a takaice, kan kwamfuta da manhajojinta. Duk da yake wannan shi ne abin da ya kamata a ce mun fara dashi, amma dokin sanin Intanet da karikitanta ne suka shagaltar da mu. Don haka tunda mun kawo wani matsayi ko mataki wajen sanin hakikanin Intanet da yadda ake tafiyar da rayuwa a kanta, dole mu koma tushe, ko mazaunin da wannan fasaha ke dogaro wajen aiwatar da dukkan abin da za mu ci gaba da kawo bayanai kansu. Wanann ya sa za mu yi bayani kan Kwamfuta, ita kanta, da kuma ruhin da ke gudanar da ita. Na tabbata daga lokacin da mai karatu ya karanta wadannan bayanai, insha’Allahu zai samu sauyin mataki, wajen fahimtar darussan da za su biyo baya. Mu je zuwa, wai mahaukaci ya hau Kura.