Shahararrun Jirage Masu Sarrafa Kansu
Akwai nau’ukan jirage masu sarrafa kansu guda 12 da suka shahara. Nau’in jirgi na farko shi ne mai suna QinetiQ Zephyr Solar Electric, wanda a halin yanzu an kiyasce cewa yayi shawagi na tsawon sa’o’i 336 da mintuna 22, wato kwatankwacin kwanaki 14 kenan tun bayan kera shi da aka yi a watan Yuli na shekarar 2010. Akwai wani makamancinshi da aka kera a watan Yuli na shekarar 2008, shi kuma ya kwashe sa’o’i 82 ne da mintuna 37 a sararin samaniya. Wannan sunansa daya ne da wanda ya gabace shi. Sai kuma nau’i na gaba mai suna Boeing Condor, wanda aka kera a shekarar 1989. Shi kuma a iya tsawon rayuwarsa yayi shawagi na tsawon sa’o’i 58 da mintuna 11 ne kacal. A halin yanzu an masa ritaya, yana can a girke a Gidan Tarihin kayayyakin sojin sama na kasar Amurka da ke Jihar Kalfoniya. Sai wani nau’in QinetiQ Zephyr da aka sake kerawa a shekarar 2007, wanda shi kuma aikin sa’o’i 54 kacal yayi. Sai nau’in IAI Heron, wanda ba a tantance shekarar da aka kera shi ba, shi kuma shawagin sa’o’i 52 kacal ya kwashe a sararin samaniya.
Akwai kuma wani nau’i mai suna AC Propulsion Solar Electric da aka kera a watan Yuni na shekarar 2005. Shi kuma sa’o’i 48 da mintuna 11 ya kwashe a iya shawaginsa. Sai kuma MQ-1 Predator da ba a tantance shekarar da aka kera shi ba. Sa’o’insa 40 ne da mintuna 5 a sararin samaniya. Sai GNAT-750 da aka kera a shekarar 1992, yana daga cikin tsofaffin jirage. Ya kwashe sa’o’i 40 ne kacal yana shawagi. Akwai TAM-5 da ya bayyana a watan Agusta na shekarar 2003. Shi kuma ya kwashe sa’o’i 38 ne da mintuna 52 a sararin samaniya. Wannan shi ne mafi kankanta daga cikin jirage masu sarrafa kansu da kasar Amurka ta kera, wadanda za a iya cilla su sararin samaniya su yi dogon zango; TAM-5 ne mafi kankanta daga cikinsu.
Sai kuma nau’in Aerosonde da aka kera a watan Mayu na shekarar 2006. Ya kwashe sa’o’i 38 ne kacal da mintuna 48 a shawaginsa. Sai wani nau’i da aka kera don daukan kayan soji mai suna Vanguard Defense. An kera shi ne a watan Fabrairu na shekarar 2011, wato shekarar da ta gabata kenan. Shi kuma ya zuwa yanzu ya kwashe sa’o’i 2 ne da mintuna 55. Tunda ba a jima da kera shi ba. Sai nau’i na karshe da za mu dakata a kansu mai suna TAI Anka da aka kera a watan Disamba na shekarar 2010. Shi kuma tafiyar kwana daya kacal yayi, wato sa’o’i 24 kenan.
Wadannan, a takaice, su ne shahararrun jirage masu sarrafa kansu da suka yi dogon zango a rayuwarsu. Akwai wadanda ake kerawa a halin yanzu da ake sa ran su kwashe watanni ko ma shekara suna shawagi a sararin samaniya wajen tattaro bayanai ko kai hari ko kuma yin dako don gano shirye-shiryen abokan gaba. Yanzu aka fara, wai mahaukaciya ta shiga gada sau tara. Wannan wani zamani ne da muka shigo da kowace kasa ke kokarin kwatan kanta a bangaren tsaro ta hanyar kwarewarta a fannin kimiyya da fasahar sadarwar zamani. Wacce bata fadaka ba kuma, ita ta jiwo, sautun mahaukaciya. Allah mana gamo da katar, amin.