
Kasuwar “Windows Vista” Tana Ƙara Dusashewa
Sanadiyyar matsalolin da wannan nau’i na babbar manhaja take dashi, jama’a da dama sun fara kaurace mata. Bayanai na nuna cewa hakika kamfanin Microsoft yayi kuskure wajen fitar da ita. Nan gaba ana tunanin zai fitar da wata babbar manhajar, don ceto kwastomominsa.