![Tsarin Fasahar Sadarwar Rediyo a Kimiyyance (1)](https://babansadik.com/wp-content/uploads/2017/03/rediyo-1.jpg)
Tsarin Fasahar Sadarwar Rediyo a Kimiyyance (1)
Bincike na musamman kan hakikanin fasaha da na’urar dake tafiyar da rediyo. Kasidun da muka gabatar a baya kan fasahar rediyo sun shafi tsarin shirye-shirye ne da yadda ake saurare. Amma wannan jerin kasidu da za mu fara daga yau, za su ta’allaka ne ga asalin fasahar dake samar da siginar rediyo, da yadda tasoshi suke samuwa, da kuma nau’ukannsu.