![Nau’ukan Fasahar Sadarwa a Intanet (4)](https://babansadik.com/wp-content/uploads/2017/03/sadarwa-a-intanet-4.jpg)
Nau’ukan Fasahar Sadarwa a Intanet (4)
A makon da ya gabata idan masu karatu basu mance ba, mun kawo bayanai kan tsarin da masu tashoshin talabijin suke bi ne wajen yada shirye-shiryensu, da kuma nau’ukan shirye-shiryen da suke da su a shafukan Intanet. Wannan mako, kamar yadda muka yi alkawari, zamu dubi hanyar sadarwa ta jarida ce da mujallu da suka mamaye giza-gizan sadarwa ta Intanet, kamar wutar daji. Har wa yau, za mu dubi irin tsarin da suke bi wajen yada labarai da kasidu da makaloli. Idan shafuka basu mana halinsu ba, zamu kawo wasu daga cikin jaridun da ke da shafukan yanar gizo a Intanet.