![Sakonnin Masu Karatu (2022) (3)](https://babansadik.com/wp-content/uploads/2018/10/Tambayoyi2.png)
Sakonnin Masu Karatu (2022) (3)
A duk sadda ka matsa alamar “Like” dake wani shafi (Page), ko karkashin wani rubutaccen sako (Text Post), ko hoto (Image Post), ko bidiyo (Video Post), za a wallafa sunanka a jerin wadanda suka ga wannan sako, kuma suka nuna sha’awarsu gareshi. Sannan wannan zai sa injin Facebook ya yi hasashen nuna maka wasu sakonni masu alaka da wanda ka kaunata. Wannan ke tabbatar da tasirin wannan alama ta “Like”! – Jaridar AMINIYA ta ranar Jumma’a, 29 ga watan Afrailu, 2022.