![Mu Leka Duniyar ‘Yan Dandatsa (Hackers) (1)](https://babansadik.com/wp-content/uploads/2017/03/duniyar-dandatsa-1.png)
Mu Leka Duniyar ‘Yan Dandatsa (Hackers) (1)
‘Yan Dandatsa kwararru ne kan harkar kwamfuta da abin da ya shafi ruhinta, masu amfani da kwarewarsu wajen shiga kwamfutocin mutane ba tare da izni ba, a nesa ne ko a kusa ; masu aiko ma kwamfutoci cututtuka da dama, don satan bayanai ko aikin leken asiri. A takaice dai mutane ne masu mummunar manufa wajen kwarewarsu. A yau za mu leka duniyarsu ne don sanin hakikanin tsarin rayuwarsu : irin sunaye ko lakubbansu, gidajen yanar sadarwarsu, shahararrun littafai kan aikinsu, dabi’unsu da addininsu na dandatsanci da kuma shahararru cikin finafinan da aka yi kan sana’arsu. Ga fili ga mai doki.