![Karantar da Ilimin Kimiyya ta Kafafen Yada Labarai](https://babansadik.com/wp-content/uploads/2017/03/kimiyya-jaridu.jpg)
Karantar da Ilimin Kimiyya ta Kafafen Yada Labarai
A wannan mako mun dubi tasirin mujallu da jaridu dake Intanet ne wajen karantar da mutane ko fadakar dasu kan ilimin kimiyya. Mun kuma dubi tsarin jaridun Najeriya wajen yin hakan ko rashinsa.
Makaloli a fannin kimiyya da fasaha!
A wannan mako mun dubi tasirin mujallu da jaridu dake Intanet ne wajen karantar da mutane ko fadakar dasu kan ilimin kimiyya. Mun kuma dubi tsarin jaridun Najeriya wajen yin hakan ko rashinsa.
A makon da ya gabata mun fara kawo bayanai kan tsarin da ke tattare da yada labarai da wakoki a gidajen yanar sadarwa na tashoshin rediyo da ake dasu a giza-gizan sadarwa ta duniya. Mun kuma nuna irin hanyoyin da su ke bi wajen taskance labaran musamman ga tashoshin FM masu sayar da wakoki ko kuma yada taskantattun shirye-shiryen su. Har wa yau, ba mu karkare wancan mako ba sai da muka tabbatar da cewa mun kawo bayanai kan dukkan makale-makalen da suka dace mai son sauraron labarai da shirye-shiryen tashoshin rediyo ta Intanet ke bukata kafin yayi hakan. A yau kuma cikin yardan Ubangiji za mu kama hanya in da za mu ji irin tsarin da masu tashoshin Talabijin ke bi a nasu harkan.
Mun fara kawo mukaddima a makon da ya gabata kan nau’ukan fasahar sadarwa da ke giza-gizan sadarwa na Intanet. Inda muka fara da irin dalilan da suka haddasa yaduwar nau’ukan wadannan hanyoyin sadarwa a Intanet, duk da cewa suna da nasu muhallin da su ke ta taka rawa shekaru kusan hamsin da suka gabata. A yau muka ce za mu ci gaba da koro bayanai kan ire-iren wadannan nau’ukan hanyoyin sadarwa, da tsarin da suke gudanuwa a kai da kuma yadda mai karatu zai iya amfana da wadannan hanyoyi ba tare da ya mallaki nau’urorin da ake sauraro ko saduwa da su ba. Bisimillah, wai an hada Malamai kokawa:
Akwai nau’ukan hanyoyin sadarwa dake cikin Intanet, kamar su talabijin da rediyo da jaridu. Daga wannan mako za mu dubi wadannan hanyoyin sadarwa, da tsarinsu a Intanet da kuma irin fasahar da suke dauke dashi.