![Tsaunuka Masu Aman Wuta (1)](https://babansadik.com/wp-content/uploads/2017/03/tsauni-1.jpg)
Tsaunuka Masu Aman Wuta (1)
Sanadiyyar wasu tsaunuka masu aman wuta da suka balbale sararin samaniyar duniya ta bangaren turai da amurka, daga kasar Ice Land, jiragen sama da dama sun kasa tashi don shawagi tsakanin kasashen dake wadannan nahiyoyi na duniya. Hakan ya faru ne sanadiyyar tokar kunun dutse (Ash Plum) da wadannan tsaunuka suka ta bulbularwa. A yau za mu fara gudanar da bincike kan yadda al’amari ya faru, da yadda tsaununaka suka kasu, da kuma dalilan dake haddasa musu kamawa da wuta.