
An Kaddamar da Dandalin “Google Plus”
A cikin ‘yan kwanakin nan ne aka kamfanin Google ya kaddarar da sabuwar manhaja mai suna: Google Plus”, wacce ake sa ran za ta zama kamar kishiya ga sauran manhajojin dandalin sada zumunta irin su “Facebook” da “Twitter” da sauran makamantansu. A wannan mako na kawo mana takaitaccen bayani ne kan bangarorin wannan manhaja, da siffofinta.