![Mazan Jiya: Muhammad Ibn Musa, Al-Khawaarizmi (6)](https://babansadik.com/wp-content/uploads/2017/03/khawarizmi.jpg)
Mazan Jiya: Muhammad Ibn Musa, Al-Khawaarizmi (6)
A makon yau mun dubi rayuwar babban Malami ne Muhammad bin Musa, wanda aka fi sani da “Al-Khawarizmi”, masani kan fannin lissafi, wanda sanadiyyar bincikensa ne aka samu asalin ilimin da ya shafi kariyar bayanai a fannin sadarwa na zamani. Shi ne kuma ya samar da fannin “Aljabru” ko “Algebra”, wanda shahararren fanni ne a ilimin lissafi.