
Bayani Kan Ɓangarorin Wayar Salula da Dalilan Tsada ko Araharta (5)
Kasancewar wayar salula na’ura ce da ake tare da ita a jiki a kowane lokaci, saboda yanayin girmanta (shi yasa ake kiranta da suna “Mobile Phone” – wato wayar da ake tafiya da ita duk inda ake), yasa batirinta na ɗauke ne da sinadaran dake iya riƙe makamashin lantarki an tsawon lokaci, sannan kuma ana iya cajin batirin lokaci zuwa lokaci. – Jaridar AMINIYA, Jumma’a, 1 ga watan Satumba, 2023.