![Tasirin Fasahar Intanet Ga Kwakwalwar Dan Adam (2)](https://babansadik.com/wp-content/uploads/2017/03/Internet-Addiction2.jpg)
Tasirin Fasahar Intanet Ga Kwakwalwar Dan Adam (2)
A makon da ya gabata ne idan masu karatu ba su mance ba, mu ka fara jero bayanai kan irin tasirin da Fasahar Intanet ke yi ga kwakwalwar dan Adam, saboda irin mu’amalar da ya ke yi da wannan fasaha. Mun yi bayanin irin dalilan da ke haddasa tasirin, da kuma cewa lallai akwai alaka tabbatacciya mai kama da kawalwalniya, wacce ke samuwa tsakanin kwakwalwar dan Adam da kuma asalin duniyar da yake ciki. Mun nuna cewa wannan alaka na samuwa ne sanadiyyar tasirin wannan fasaha da kwakwalwar mai mu’amala. Daga karshe mu ka yi alkawarin kawo abin da hakan ke haifarwa, da yadda za a iya magance wata matsala idan akwai. Saboda yanayin tsarin da bayanan su ka zo, mun ce mai karatu ba zai fahimci in da aka dosa gaba daya ba, sai a wannan mako. Mu na kuma fatan hakan. Don haka yanzu za mu ci gaba.